Nijeriya tabada mahimmanci wajen samar da ruwansha mai tsafta Inji Ministan Ruwa

Nijeriya tabada mahimmanci wajen samar da ruwansha mai tsafta
Inji Ministan Ruwa

Daga Zubairu M Lawal

Ministan ruwa na tarayyar Nijeriya Alhaji Sulaiman Adamu ya yabbaya yadda Gwamnati ta dukufa wajen samar da ruwansha mai tsafta domin inganta rayuwar alumman qasa.

Ministan yayi bayanine a bikin ranar Ruwa ta Duniya a shekarar 2019, mai taken mugudu tare mu tsira tare.

Najeriya tabi sauran Kasashen Duniya wajen gudanar da mahimmiyar bikin da kuma wayar dakan alumma saboda amfanin tsaftacecen ruwansha mai tsafta ga Xan Adam.

Ministan ya bayyana cigaban da aka samu a wanan lokacin dagane da harkan ruwa.

Yace; “Wani abun burgewa shi ne yadda Najeriyan ta bude dandalin Yanar Gizo dan gudanar da aiyukan wayar da kan Al’umma wajen ammfani da tsaftatancen Ruwan shan dan ya zama sun cimma kudirin da ake so akai na Duniya a 2025”
Yace; adireshin da muke amfani da ita kamar haka www.cleannigeria , duk wanda yake bibiyarta zai tarar da yadda muke nunatar da alumma yadda zasuyi amfani da basirar samar da tsaftacecen ruwansha.

Wanan duk yana cikin jerin abubuwan cigaba da Gwamnatin Nijeriya ta sanya domin inganta rayuwar alumma.

Ya kara da cewa Gwamnati na kashe makudan kudade wajen bunqasa harkokin noma domin samun ingantaciyar abinchi wadatace a qasa.

Kuma tana kula da duba magudanar ruwa da muke dasu a wasu jihohinmu . mu qara inganta su saboda baiwa manomarmu damar samun gulaben da zasuyi amfani da ruwa wajen gudanar da nomar rani.

Gwamnati ta himmatu tare da kungiyoyin kula da harkokin noma masu zaman kansu saboda baiwa manoma mahimmanci domin bunkasa harkan noma. Gwamnati ta baiwa manoma rancen kudade da kayayakin noma wanda zai taimaka masu wajen kara himma kan aikin gona.

Gwamnatin tarayyar ta yabawa kungiyar kula da yara qanan wato UNICEF yadda take bada mahimmanci wajen wayar da kan alumma masamman iyaye ta yadda zasu riqa shayar da yara tsaftaceciyar ruwa.

Haka zalika tana kara shiga ga Gwamnatochi domin basu ingantaciyar shawara wajen yadda zasu riqa samar da tsaftaceceuar ruwansha ga alummansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *