Sabon salon sanatan mutani a Babur
Daga Ibrahim Lawal
Ana cigiyar Iyaye ko ‘yan’uwan wannan baiwar Allah mai suna Lubna wadda aka tsince ta jiya Juma’a (19/04/2019) a garin Keffi da ke Jihar Nasarawa.
Acewar Lubna ta hau acaba ne kawai sai ta tsinci kanta a Keffi. Sannan ta bayyana Amina a matsayin mahaifiyarta, kuma tana da kannai hudu da yayyi biyu. Iyakar abin da ta iya tunawa kenan.
Don haka, duk wanda Allah ya sa ya waye ta, ana iya zuwa MALONEY FM KEFFI don karin bayani, ko kuma a tuntubi lambar waya 07060562283.
Da fatan Aallah Ya sa a dace.