Bayan karbar Miliyon 500 Malaman Izala sunje yawon Gantali a Amurka
Daga Aliyu Mustapha
Malaman Izala sun tafi kasashen waje yayin da ake cikin mawuyacin hali
Mun samu labari cewa shugabannin kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa’ikamatus Sunnah na JIBWIS wanda aka fi sani da Izala sun harba zuwa kasar Amurka jim kadan bayan babban zaben 2019
Jaridar Desert Herald ta soki ziyarar da Malaman Izala karkashin jagorancin Abdullahi Bala Lau su ka kai zuwa Amurka a daidai lokacin da Mabiyansu ke cikin wani mawuyacin hali a kusan kowane bangare na Najeriya.
Idan ba za ku manta ba, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya nuna goyon bayansa ga a fili ga takarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019, yayin da Sakataren kungiyar watau Kabiru Gombe ya rika caccakar ‘Dan takarar PDP.
Jaridar ta zargi shugabannin wannan kungiyar addini na reshen Kaduna da karbar kudi daga hannun jam’iyyar APC wanda ya sa su ka rika sukar Abokin takarar shugaba Buhari watau Alhaji Atiku Abubakar babu kaukautawa.
Muhammad Kabir Haruna Gombe a ofishin Majalisar dinkin Duniya
Desert Herald tana zargin Sheikh Bala Lau da kuma Muhammad Kabir Haruna Gombe da karbar sama da Naira Miliyan 500 da kuma manya motoci daga hannun wasu manyan APC irin su gwamnan jihar Adamawa Jibrila Bindow.
An kuma zargi manyan kungiyar da karbar motoci daga hannun wani gwamnan Arewa maso yamma a lokacin da ake yakin zabe. Jaridar tace Malaman kungiyar sun buge ne da sanya tufafin takama da motoci a maimakon aikin addini.
Rahotannin su ke cewa Bala Lau ya zabi ya tafi kasar Amurka ne a lokacin da Musulmai ke fama da ‘dan karen wahala. An dai ga Kabir Gombe cikin hotuna yayin da yake shakatawa a wurare dabam-dabam a cikin kasar ta Amurka.