Yadda aka zalunci alumman Afirka lokacin cinikin bayi – Guterres

Yadda aka zalunci alumman Afirka lokacin cinikin bayi
– Guterres
Daga Zubairu M. Lawal

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya nuna matukar takaicin shi akan yadda aka rinka kasuwancin na zaluncin mutane a matsayin bayi daga yankin Afirka zuwa kasashen Turawa.

Yace; Babban al’amarine wanda tarihi ba zai taba mantawa da shi ba a Duniya baki daya.

Guterres ya baiyana hakan ne a sakon shi na ranar bukin tunawa da da mutanen da aka maida su bayi da aka gudanar a wannan shekaran na 2019.

Yace; an gudanar da cinikin bayi bisa hanyoyi mara tushe inda aka rika bautar da alumman yankin Afirika a matsayin mutani marasa yanci a Duniya.

Banga abinda cinikin bayi ya qarar dashi a Duniya ba face cin zarafi da bautar da marasa galihu. An rika cinikayyar mutani a gabar teku zuwa kasashen Turai kamar ana safarar kaya.

Babu abinda ake gudanarwa ga bayi face aikin wahala da bauta da zalunci. Maimakon a karantar dasu su samu ilumi sai aka bautar dasu suka koma bayi.

Hakiqa cinikayyar bayi ya haifar da cibaya a nahiyar Afirika .

A shekara 400 nahiyar Afirika ta kasance cikin qangin bauta da rashin yanchi inji Sakataren Majalisar Dinkin Duniya a sakon da ya aikae zuwa cibiyar yada labarin na Majalisar.

Shima da yake jawabi Dakta Oluseyi Soremekun Babban jami’i a ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Nijeriya yace; hakika wanan lamarne da alumman nahiray Afirika dama Duniya bazata manta da shiba.

Dole a rika tunawa da abubuwan da suka faru ga alumman Afirika a ranakun 25 ga watan uku na kowane shekara domin sanar da alumma yadda illar ciniken bayi ya haifar a Afirika.

Miliyoyin Jama’a daga yankin Afirika maza da mata da yara kanan sun dandana bakar wahala a wanan lokacin da ake kama mutani a matsayin bayi ana zuwa dasu kasashen Turai an bautar dasu ga bakar yunwa .

Wasu dagana sun tafi ke nan sai a lahira ,alumma dadama sun rasa danginsu ta hanyar cinikin bayi.

A wani gamayyar taron bita da cibiyar yada labarai na Majalisar Dinkin Duniya dake birnin Lagos ta gabatar da ilumin yadda duniyar Afirika ta kasance taron da ya shafi Dalubai da malamai da Sarakunan gargajiya da sauransu.

Taron ilumin ya hada mutani daga bangarori dabam dabam na alumman cikin gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *