Bukola Saraki ya zama Manzo na masamman a Duniya

Hukumar kare hakkin dan Adam ta duniya ‘IHRC’ ta baiwa Saraki aikin jakandancinta na musamman
Hukumar dake rajin kare hakkin bil adama ta duniya ta baiwa shugaban majalissar Dattijai, Dr Bukoula Saraki aiki a matsayin babban jakadanta na duniya.
Sanarwan da ta fito daga ofishin yada labaran shugaban majalisar, tace hukumar ta aikewa Sarakin takardar neman yardar shi kan aikin da hukumar tin ranar 16 ga watan Maris din 2019.
“A cikin wata wasika da aka aike ranar 16 ga watan Maris, Babban jami’in Diplomasiyya na Najeriya da wasu kasashen Afrika, Ambasada Friday Sani, ya ce, bisa amincewar sakataren hukumar IHRC, an nada Dr. Bukuola Saraki a matsayin daya daga cikin jakadunta mai girma kuma na musamman.”
Aikin Saraki ga hukumar zai kasance shine wanda zai jagoranci tawagar jami’an Diplomasiyyar hukumar a ayyukan da zata gudanar na duniya baki daya.
Dr. Saraki ya sanya hannu a takardar shaidar amincewa da aikin da hukumar ta bashi.
Ya kuma nuna jin dadinshi da godiya bisa aikin da hukumar ta bashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *