Dubban alumma a jihar Bauchi zasu samu lafiya kyauta
Inji Dakta Haruna Kigbu
Daga Zubairu M Lawal
Jagoran tawagar kwararun Likitocin bada agaji na kiwon lafiya da akewa kira da Gidauniyar (Doctors on the mover Africa) Honorabul Joseph Haruna Kigbu ya bayyana haka ga manema labarai a garin Bauchi.
? ¿
Jagoran tafiyar wanda akewa laqabi da Likitan Talakawa , yace akalla ana saran samada mutum dubu goma zasu amfana da wanan shirin da ke gudana a Asibitin Abubakar Tafawa Balewa dake cikin garin Bauchi a yanzu haka.
Yace; Dan Majalisar tarayya Honorabul Yakubu Dogara ya dauki nauyin wanan aiki. Yace; Yakubu Dogara ya himmatu wajen ganin alumman mavebarsa sauna samun kiwon lafiya akai akai .
Yanzu haka an raba wanan tawagar ta Likitochin gida biyu akwai wadanda suke yankin Karamar Hukumar Liman Katagun wanda ake gabatarwa a garin Azare.
Ya kara da cewa wanan aikin zai gudanane na tsawan kwanaki shida . da aka tambayeshi game da ayyukan da za’a gudanar a wanan gurin.? Yace; shi aikin kiwon lafiya akwai fannoni dabam dabam.
Saboda haka akwai vangaren masu duba cutar IDO idan yakai sai anyi aiki sai ayi idan kuma maganine ko madubi sai a bada.
Sanan akwai Ma’aikata masu cire Qabar ciki da Gyambo da masu kula da matsalolin mata.
Akwai masu gwajin cutar Kanjamau da Maleriya da sauransu. Ya kara da cewa ko a wancan karon kafin zabe ya Yakubu Dogara ya kawo mu mun gudanar da wanan shirin na kiwon lafiya inda muka kwashe kwanaki goma kuma samada mutum dubu goma sha takwas ne suka amfana da wanan shirin.
Wakilinmu da ya kasance a Babban Asibitin yaga ganewa idanunsa yadda dubban mata da maza da yara qanana sukariqa tururuwa zawa Asibitin suna karban magani .
Asibitin ya kasance babu matsaka isnke saboda halin da ake ciki na fama da rashin lafiya da kuma rashin kudade da mutani zasuje Asibitin kudi ko na Gwamnati domin duba lafiyarsu .