*An raunata tare da kama da dama, yayin da ‘yansanda suka bude wuta kan masu muzaharar Qudus*

TAKARDAR SANARWAR MANEMA LABARAI

*An raunata tare da kama da dama, yayin da ‘yansanda suka bude wuta kan masu muzaharar Qudus*

Rahotannin da suka riski Harkar Musulunci a Nijeriya daga garin Kaduna sun nuna cewa mutane da dama ne suka sami raunuka sabili da bude wutar da ‘yan sanda suka yi yayin da ake gudanar da muzaharar Ranar Kudus ta duniya, wanda a yau ake yin sa a duk fadin duniya. Sun kuma kama wasu masu muzaharar da ake yi don nuna goyon baya ga Palasdinawa raunana.

Tun da safiyar ranar yau Juma’a ne aka ga jami’an tsaro ‘yan sanda da yawa cikin shirin yaki suna fatiro a manyan titunan garin Kaduna tun kafin ma a fara muzaharar.

Jim kadan da fara muzaharar kuwa, sai ‘yan sanda rike da muggan makamai suka bude wuta ba tare da wani gargadi ba da tiyagas da harsasai masu rai kan mai uwa-da-wabi. Wannan ya jawo rudami da guje-guje a manyan titunan tsakiyar birnin na Kaduna.

Bayan nan an gan su suna kakkafa shingaye da tattare tituna da karkatar da ababen hawa daga tsakiyar birnin.

Ya zuwa lokacin fitar da wannan sanarwar, ba a san takamaime mutane nawa ne ‘yan sandan suka raunata ko kama ba, amma dai matakin da ‘yan sandan suka dauka ya dakatar da zirga-zirga a tsakiyar garin.

An ji mutanen gari da yawa suna yin tir da abin da ‘yansandan suka yi, suna masu cewa ai wannan ba shi ne karon farko da ake yin muzaharar Kudus lami lafiya a garin Kaduna ba, don haka me ya sa ‘yansanda za su kawo hari, alhali sai a neme su a rasa idan aka ce ga mahara ko masu garkuwa da mutane suna kawo hari, amma sai a gan su cikin shirin yaki in an fito muzaharar lumana?

Wannan muzaharar ta tunawa da Ranar Kudus an yi ta a ko’ina a fadin kasar nan lami lafiya in banda Kaduna, inda Gwamnan jihar ke cikin shirin zubar da jinin mutane a cikin watan Ramadan mai tsarki.

Don haka, wannan Gwamnan ne ke da alhakin duk wani mummunan abin da ya sami jama’ar da suka fito muzaharar lumanar.

SA HANNUN:

IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI
HARKAR MUSULUNCI A NIJERIYA
31/05/2019

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *