Gwamnan Sokoto yayi doka kan kiwon lafiya
Daga Aliyu Mustapha
Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto ya rattaba hannu kan wasu kudirorin dokoki guda hudu.
Kudirorin kun hada da Dokar kafa Asibitin Koyarwa na Murtala Mohammed da Cibiyar Lafiya Bai Daya na shekarar 2019.
Sauran sun hada da na kafa Kwallejin Horas da Ma’aikatan Jinya a Asibiti da Cibiyar Kulawa da Harkokin Kiwon Lafiya na JIhar Sokoto na shekarar 2019.
Sanawar da ta fito daga Dirkta Janar na Yadda labarai da Hulda da Jama’a na gwamnan, Abubakar Shekara ta ce sabbin dokokin za su taimaka wurin kawo cigaba a fanin kiwon lafiya a jihar.
“A baya, gwamnatin Tambuwal ta bayyana niyyar ta na kafa asibitin koyarwa a jihar ta yiwa wasu dokoki garambawul domin inganta fanin kiwon lafiya a jihar,” inji shi.
Ya kara bayanin cewa dokar Asibitin Koyarwa na Murtala Mohammed zai bayar da damar kafa kwamitin direktoci da babban direktan harkokin kiwon lafiya daga hukumomin masu alaka da kiwon lafiya domin tafiyar da harkokin asibitin.
Ya kara da cewa Kwallejin Nazarin Aikin Jinya zai rika koyar da kwasa-kwasai da na Satifiket, Diploma da Digiri tare da bayar da damar gudanar da bincike kan Kimiyyar Aikin Jinya.