DUK DUNIYA – Musulmai a Nijeriya sun goyi bayan Palastinu

Musulmai a Nijeriya sun goyi bayan Palastinu

Daga Aliyu Mustapha

Dubban dubatan alumman Musulmai a garuruwa da dama kusan jihohin 20 suka gudanar da Muzahara Qudu a fadin Nijeriya domin nuna goyon bayan su ga alumman Palistinawa.

Yau a fadin Duniya ana gudanar da Muzaharar Qudun domin nuna goyon bayan ga alumman kasar Palastinu da Gwamnatin kasar Isra’ila ke kashewa.

Musu Muzaharar suna rera wakoki na nuna goyon bayan ga alumman kasar Palastinu da nuna rashin amincewarsu da mamayar Masallacin Qudus wanda  Gwamnatin Harantaciyar kasar Isra’ila ke yi.

Haka zalika masu gudanar da Muzaharar suna nuna rashin amincewa da cigaba da tsare Sheakh Ibraheem Zakzaky wanda Gwamnatin Nijeriya karkashin jagorancin Muhammad Buhari keyi tsawan shekaru uku bayan kisan gillar da akayiwa dubban yan uwa Musulmai almajiran Sheakh Zakzaky a garin Zaria.

Shun cigaba da rera wakokin rashin amincewa da Zaluncin Gwamnatin Isira’ila da Gwamnatin Nijeriya. Suna kira ga Gwmnatin da tabi ummurnin Kotu na cewa a saki Sheakh Zakzaky, saboda yaje ya yi jinya sakamakon har ya zuwa yanzu akwai harsasai a jikinsa tare da iyalanisa kuma anki bari su je ganin Likita.

A garuruwan da dama a fadin Nijeriya an gudanar da Muzaharar lafiya harda Abuja amma a birnin Kaduna Gwamnatin jihar Kaduna ta farwa masu Muzaharar ta budemasu wuta da harsashi mai rai.

Harbe harben da akayi a Kaduna ya janyo zubda jinin dadama daga cikin Mata da yara qananan masu Muzaharar , ya zuwa lokacin hada wanan rohoto ba a kididige adadin wadanana suka rasa ransu da masu rauni ba.

Wannan harbe harben an yishine a tsakiyar garin Kaduna bayan Musulmai masu Muzaharar suna tafiya cikin lumana daga Abekuta road suka taso a Masallacin Yorbawa , batare da tukallar kowa ba , a dai dai Randabot na Leventis Jami’an tsaro suka bude masu wuta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *