SAKON GAGGAWA DAGA MABIYA ZAKZAKY A NIJERIYA

SANARWAR MANEMA LABARAI

*Duk wani yunkuri na amfani da tashin hankali a Abuja da sauran wurare ba da yawunmu ba ne*

Harkar Musulunci a Nijeriya ta lura da wasu wallafe-wallafe da ke karakaina a shafukan sada zumunta na zamani da ke ikirarin cewa daga Litinin 01/07/2019, Abuja za ta fuskanci gagarumin tashin hankali yayin muzaharorin neman a saki Shaikh Zakzaky da aka dade ana yi. Dangane da haka, muna fadi da babbar murya kuma a sarari cewa, ba ruwanmu da duk wata barazanar yin amfani da tashin hankali a yayin da muke neman a saki Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenah Ibrahim da sauran ‘yan’uwa musulmi da gwamnati take tsare da su dangane da kisan kiyashin Zariya na watan Disamban 2015.

Mun fada sau shurin masaki, kuma mun nuna a aikace a tsawon shekarun nan cewa, amfani da tashin hankali da kuma yin barazana, da ba da wa’adi, ba halinmu ba ne, kuma bai taba zama daya daga cikin hanyoyin da mukan bi don cimma muradunmu ba. Hakan kuma ba zai sauya ba.

Yadda muka rika bin hanyoyin lumana a fafutukarmu na neman ‘yancin Shaikh Zakzaky a tsawon shekaru tun bayan kisan kiyashin da gwamnati ta shirya kuma ta aiwatar ya isa ya tabbatar da cewa, mu ba ‘yan tashin hankali ba ne, duk kuwa da irin girma ko munin takalar mu da aka yi.

Shaikh Zakzaky bai taba yin kira zuwa ga tashin hankali ba, don haka duk wanda aka ga yana bin tafarkin tashin hankali ba zai kasance daga cikin mu ba. Ta yiwu gwamnati ce kawai ke neman shafa wa Harkar Musulunci kashin kaji, don su samu hujjar kare gazawar Buhari a dukkan bangarorin mulkin kasar nan.

Amma muna so jama’a su sani cewa, za mu ci gaba da muzaharorinmu na lumana, tare da bin duk wata hanya ta lumana da ta dace don neman a yi mana adalci, kamar yadda muka saba yi har sai mun fallasa irin munanan cin zarafin ‘yan kasa da gwamnatin nan take yi. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen neman hakkokinmu, wadanda hatta tsarin mulkin kasar nan ya kare mana su.

A karshe, muna kara yin kiran a gaggauta sakin Jagoranmu Shaikh Zakzaky da matarsa, wadanda halin rashin lafiyarsu a kullum kara tabarbarewa yake yi, musamman irin guban da aka ruwaito an yi yunkurin sa musu a yayin da suke tsare, baya ga guban da ke jikinsu na burbushin harsasan da aka harbe su da su. Kasantuwarsu cikin koshin lafiya abu ne mai matukar muhimmanci a gare mu, kuma Buhari za mu dora wa laifin duk wani mummunan abin da ya sami Shaikh Zakzaky da matarsa.

SA HANNUN:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA HARKAR MUSULUNCI A NIGERIA
Skype: Ibrahim.musa42
30/06/2019

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *