SAKON YAN SHI’A – *Mutum 3 sun sake mutuwa a tsare gun ‘yansanda* Inji IMN

*Mutum 3 sun sake mutuwa a tsare gun ‘yansanda*
Inji IMN

Daga Abdullahi Yusuf

Wasu rahotanni da suka riski Harkar Musulunci a Nijeriya sun tabbatar da cewa, wasu karin mutum uku da aka harba sun yi shahada a yayin da suke tsare a hannun ‘yansanda a ofishinsu na SARS da ke Abuja tun ranar Litinin 22/07/19. Sun yi shahadar ne a ranar Laraba 24/07/19 a dalilin harsasan da suka raunata su a yayin muzaharar neman a saki Shaikh Zakzaky da aka yi a farkon makon nan.

Ba wannan ba kawai, wasu na iya rasa rayukansu a tsare, saboda akalla mutane 15 da suke da raunuka na harbin bindiga ke tsare a wannan mugun wuri na tsare jama’a ba tare da ana kula da lafiyarsu ba. A cikin su ma har da mata da kuma wani karamin yaro da aka harba a kafa.

Duk wani yunkuri da ‘yan’uwan wadanda ake tsare da su suka yi don ganin ‘yan’uwansu sun sami magani bai yi nasara ba, al’amarin da ke nuna Hukumomin na jiran wadannan majinyata ne kawai ta Allah ta kasance a kansu.

Abin takaici ne da ya zamana cewa duk wani abu, in dai dangane da wadanda ake ce wa ‘yan Shi’a ne, to jami’an tsaro sukan manta da duk wata ka’idar aiki ta kasar nan da ta kasa da kasa, su rika nuna mugun keta da dabbanci, kamar yadda suka yi wa wani dan’uwa musulmi a ranar Laraba da aka tsince shi yashe a gefen titi, bayan sun azabtar da shi, tare da watsa masa tafasasshen ruwan zafi a jikinsa.

Don haka muna kira ga al’ummun kasa da kasa da ‘yan rajin kare hakkin bil’adama da kungiyoyinsu da su ziyarci wannan wuri na tsare jama’a na SARS da ke Abuja, inda ake tsare da ‘yan kasa a wani mummunan yanayi.

Muna kuma kira ga Hukumar ‘yansanda da ta mika mana wadanda suka raunata kuma take tsare da su don saboda a samu a ceto rayukansu. Haka nan kuma muna so a hannunta mana gawawwakin ‘yan’uwanmu da aka kashe tun ranar Litinin don mu yi musu janaza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Hukumar ‘yansanda ta sani cewa, yi wa mutane kabarin bai-daya mummunan laifin yaki ne, wanda ya kamata su ji tsoron aikata hakan, ko don gaba.

SA HANNU:

IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA HARKAR MUSULUNCI A NIJERIYA
Skype: Ibrahim.musa42
26/07/2019

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *