Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan kisan qananan yara a Nijeriya
Daga Zubairu Lawal
Majalisar Dinkin Duniya tayi Allah wadai da hare haren Ta’addanci da ake kaiwa kan yara qanana a yankin Maiduguri dake yankin Arewa maso gabashin Nijeriya.
A ranar 16 ga watan da yagabatane aka kai harin Ta’addanci kan farafren hula dake Kauyen Mandarari dake qaramar hukumar Koduga cikin jihar Barno.
Harin da yayi sanadiyar asarar sama da mutum 30 cikin su harda yara qanana . Kauyen Mandarari yanada nisan kilomita 40 tsakanin sa da babban birnin Maiduguri.
Da yake nuna alheninsa da muryan Majalisar Dinkin Duniya Mista Edward Kallon yace ; yan ta’adda basu da tausayi basu da imani saboda suna kisan fararen hula wadanda basun hawaba bare sauka.
Yace; yara qanana suna da rawar da zasu taka na cigaban qasa amma haka kawai , ake kai hari ana kashe su ba tare da nuna tausayi ba.
Ya qara da cewa Mata da suke gudanar da ayyukan jinkai suma basu tsira ba daga yadda yan ta’addan ke kashe su ko su kwashesu zuwa daji domin yimasu aikin bauta.
Yace ; yanzu haka alumman da suke cikin halin jinya suna buqatar magani a Asibiti.
Ana kai hare hare guraren da farafren hula ke haduwa su gudanar da ayyukan su na cigaba kamar kasuwa da filayen wasannin.
Idan mutum yana kallon ire iren wannan ko a akwatin talabijin abin yakan bada tausayi.
Wasu kaga an raunatasu da bama bamai ko harsasai. Yace; a shekarar 2018 an samu asarar rayuka yara qanana 289 wadanda harin Ta’addanci ya kashe.
Yace; Majalisar Dinkin Duniya tana nuna matukar damuwa da irin zaman kunci da Iyaye mata suke kasancewa a sansanonin YAN gudun hijira sakamakon yadda harin Ta’addanci ke rabasu da muhalinsu