Batun zaman lafiya Fulani sun jinjinawa Gwamnan Benue da na Nasarawa
Daga Zubairu Lawal
A ranar lahadine tawagar kungiyoyin Fulani suka ziyarci Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule a garin Lafia.
Da yake jawabi Gwamna Abdullahi Sule ya yaba da wanan ziyarar da tawagar Fulani suka kawo masa na masamman. Yace; na lura naga akwai matsala tsakanin mutanin jihar Benue da Fulani kuma gashi Fulani suna gudanar da kiwo a Nasarawa amma basuyi a Benue wannan dalilin yasanya nayi tattaki zuwa jihar Benue inda na samu Gwamna Samuel Oton muka tattauna game da batun Ruga.
Yace; duk da cewa Gwamna Oton yana da ikon aiwatar da dokar da zai samarwa alumman jihanshi zaman lafiya amma na rokeshi game da wanan matsalar saboda kowa ya zauna lafiya.
Na nunatar dashi cewa suma Fulani akwai dayawa da yan asalin jihar Benue ne.
Yace; duk da cewa kowani Gwamna da yadda yake daukar lamarinsa amma babu wanda baya buqatar zaman lafiya.
Gwamnan ya qara da cewa” tun kafin Gwamnatin tarayya ta ayyana batun samar da Ruga naje nayi binchike game da shirin”
Yace; ” na tara Sarakuna na sanar dasu ga yana yin tsarin ruga yadda zamuyi zamu samar da guraren makiyaya guda dari. Ciki harda makarantu da kasuwa da wajen ansan maganin dabbobi da wajen abinchin dabbobi, dama wajen yanka dabbobi”.
Ya qara da cewa shiyasa koda aka samu akasi da Gwamnatin tarayya tace ta dakatar da shirin to mu muna nan zamu aiwatar da namu shirin koda kadanne.
Da yake jawabi a madadin duk kanin kungiyoyin Fulani
Sarkin Fulanin jihar Nasarawa Sanata Wali Jibirin ya yabada zaman sulhu da akayi tsakanin Gwamnoni biyu na jihar Nasarawa da jihar Benue.
Yace; taron na Gwamnnonin biyu ya mai da hankaline ,wajen yadda za’a samar da zaman lafiya a tsakanin manoma da makiyaya , da alumman jihohin biyu baki daya.
Sanata Wali Jibirin ya furta hakane a lokacin da tawagar Fulani da kungiyoyin su dabam dabam suka ziyarci Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule a ranar Lahadi.
Duk da cewa Sarkin Fulanin shine Shugaban Amintattu na jam’iyyar PDP ta qasa amma cewa yayi bai ziyarce Gwamnan a matsayin Harlan psiyasa ba sai xan cigaban qasa.
Yace dole mu yabawa Gwamna Abdullahi Sule saboda yadda suka ya karbi shirin nan na samar da Ruga . yace; mu alumman Fulanin jihar Nasarawa muna bada goyon baya da wanan shirin.
Yace; rashin Labin shabu da gandun daji ya sanya yanzu haka ake samun sabani tsakanin sauran alumma da makiyaya. Yace; yanzu makiyaya da yawan dabbobi da yawan manoma sun qaru amma akwai matsalar wuraren kiwo.
Ya qara da cewa ; idan aka samar da Ruga zai taimaka wajen ilimantar da yaran Fulani saboda zasu samu damar zama a waje daya suyi karatu.
Sanata Wali yayi kira ga Shugabannin kungiyoyin Fulani dasu watsar da rigingimun Shugabanci dake tsakaninsu su hada kai wajen magace matsalar rashin tarbiyan yaransu da suka bachi da shaye shaye da satan shanu da yin Garkuwa da mutani.
Wali yace ; suna shiye -shiryen zagayen ganawa da Gwamnonin qasan nan 36 saboda su nuna masu mahimmancin yin Ruga sabanin inda suke tunanin matsalar.