Manya kungiyoyi sun dukufa wajen wayar dakan alumma domin zaman lafiya a Nijeriya

Manya kungiyoyi sun dukufa wajen wayar dakan alumma domin zaman lafiya a Nijeriya

Daga Zubairu M Lawal

Kungiyar tarayyar Turai da hadin giwar majalisar Dinkin Duniya, sun fara aikin hadin giwa na wayar da kan mutane a kan zaman lafiya a Lagas da Yola.

Taron wayar da kan dai wanda suka faro shi a Calaba, jihar Cross River, Lagas, da kuma Jihar Adamawa. A taron dai suna bayyana ma Al’umma ne akan yadda za’a fahimci juna wajen yin mu’amalar yau da kullun, wanda ta haka ne kawai za’a sami dauwamamman zaman lafiya a Nijeriya.

Taron yana gudanane a zauruka inda ake gyayyato alumma masu yaruka dabam dabam dama mabambamtan addinai.

Taron da ya gudana a garin Yola dake jihar Adamawa ya samu halartan Shugabannin qabilu dabam dabam tare da dumbin magoya baya.

Gwamanan jihar Adamawa Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri,
Yace; zai gina jihar Adamawa ta mahimmiyar hanyar da alumma zasuji dadin rayuwa. Zai samar da kayayakin more rayuwa zai baiwa mata da maza da matasa aikinyi masamman masu rayuwa a karkara .

Gwamnan Fintiri wanda Sakataren Gwamnatin Alhaji Bashir Ahmed, ya wakilta. Yace; cigaban mata da matasa shine hakikanin zaman lafiya da duk Duniya ake buqata.

Sannan yayi magana ne kan yadda mutani zasu riqa girmama juna da mutunta al’adun juna dama addinan juna. Saboda wanan hanyar CE kadai zai tabbatar da fahintar juna har a samu zaman lafiya.

Taron da ya gudana a garin Calabar Babban birnin jihar Cross River ya samu halartan manyan yan siyasa da masu fada aji ciki harda Muqaddashin Gwamnan jihar Farfesa Ivere Esu.

Da yake jawabi a madadin Gwamnan jihar Muqaddashin Gwamnan yace; hanya dayace alumma zasubi domin samun zaman lafiya shine hadin kai da hakuri da juna. Yace; duk cikanmu mutanine amma kowa da irin hankalinsu da ilumin da ya samu a rayuwa.

Yace; idan zamuyi koyi da rayuwar magabata yadda sukayi hakuri da juna suka mutumta juna sukayi nasarar samar da dangantaka ta hanyar zaman tare.

Yace; a rayuwa ba lallaine abinda kakeso shine matarka zatayi ba to ina kuma ga alumma da kuke tare?.

Ya qara da cewa; wanan hanyar da Majalisar Dinkin Duniya ta qirqireshi shine ginshikin samar da zaman lafiya a Nijeriya.

Da take jawabi a madadin Gwamnatin jihar Lagos Babban Sakatare a Ma’aikatan Mata da walwala ta jihar Lagos.Mrs Yewande Falugba tace; kamar yadda Gwamnatin jihar Lagos tayi dogon nazari wajen gani ta bunqasa harkokin mata a jihar, shine babban cigaba mai dorewa.

Saboda mata sune cigaban kowata alumma domin suke kula da yara su basu ingantaciyar tarbiya su koyar dasu girmama na gaba kowanene.

Idan mata suna da xan sana’arsu a hannu zasu taimakawa rayuwar yaransu su kuma basu tarbiya ta yadda zasu taso cikin walwala da jin dadi.
Falugba,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *