WANJAMI ZAYASON JARFA – IZALA TA SOKI BBC KAN DANGANTATA DA JAGORAN BOKO HARAM.
Daga Aliyu Mustapha
Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah tana Allah wadai da kalaman da sashin Hausa na BBC suka watsa akan cewa Tsohon madugun kungiyar Ahalil Sunna lidda’awati wal jihad wanda akafi sani da Boko Haram, Ustas Muhummadu Yusuf yayi karatu a jami’ar musukunci ta Madina, Wanda wadannan kalamai ba gaskiya Bane inji shi.
Kamar yadda muka ruwaito daga bakin shugaban kungiyar ta kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, yace wanda ya ruwaito wannan labari ya nuna rashin kwarewar aiki gareshi, Ansan Dan Jarida da binciken kwakwaf kafin hada rahoto, amma hakan bai samu ba ga Wanda ya ruwaito wannan labarin.
Kamar yadda Malam Masur Sokoto ya wallafa a shafinsa, Akwai mamaki matuka irin yadda tashar BBC Hausa Radio ta wallafa tarihin jagoran kungiyar Boko Haram Ustas Muhammad Yusuf jiya a shafinta, bayan ya cika shekaru 10 da mutuwa tare da alakanta shi da Jami’ar Musulunci ta Madina.
Wannan ba zai yiwu ya zama kuskure ba. Musamman in muka yi la’akari da yadda a cikin rahoton suka yi biris da kasancewarsa jagoran Zakzakiyya na jihar Yobe kafin ya rungumi kungiyar Tajdid, sannan ya sauya sheka daga baya zuwa abinda aka kira Salafiyya, da kuma yadda BBCn suka fito da sunan Ibnu Taimiyyah baro baro a matsayin wanda Muhammad Yusuf yake da’awar koyi da shi. Amma abin tambaya shi ne: Don wace manufa suka yi haka?
To, ko don mine ne dai muna sanar da su cewa, al’ummar kasar Hausa ta ga alheran wadanda wannan Jami’a mai albarka ta yaye a tsawon kusan shekaru 60 da ta yi tana hidimar karantar da yayan Musulmin duniya sahihin karatun addinin Musulunci kyauta.
Kuma Alhamdu lillahi ba a san dan ta’adda ko daya wanda ita wannan Jami’ar ce ta kyankyashe shi ba. Muhammad Yusuf kuma ko bangon Jami’ar bai taba gani ba.
Sai dai wanan Labarin da kungiyar ta Izala take musantawa ,tanayine da ganga saboda taga Muhammad Yusuf daga cikin ta yake kuma kungiyar Boko Haram daga Izala tafito, inji Musa Abdullahi Kano da ya wallafa a shafinsa na Twitter. Inda ya kara da cewa kowa yasan Muhammad Yusuf tare yake da Marigayi Jafar Adam tsawan Shekaru.
Itama Fatima Arafidi cewa tayi asai wanzami bayason jarfa , “nayi mamaki da yau IZALA kecewa yan Jarida basuyi bincike ba to su Bala Lau da suke yada karya da sunan gaskiya alhalin karyane ”
” ta qara da cewa Bala Lau yace yan Shi’a suna da alkur’aninsu dabam kuma yan ta’addane wanda haryau bai taba nuna kur’anin yan Shi’a ba”
Shima Bala Musa Minna cewa yayi , ai Jami’ar Madina nane cibiyar yaye yan Ta’adda . kuma ba’a taba samun yan Ta’adda a Shi’a ba , sai dai a IZALA.