KO KUNSAN – WANI GWAMNA YABAIWA MA’AIKATA KUDIN HUTU SUYI BUKIN SALLAH
Daga Zubairu Lawal
Maigirma Gwamnan jihar Jigawa Abubakar Badaru ya sanya an biya kudaden hutu domin ma’aikatan jihar suyi bikin Sallah cikin wal-wala.
Shugaban Kungiyar kwadiqo NLC sunusi Suleiman maigatari. Yace wannan kudin hutu zai sanya farin ciki cikin zuciyar ma’aikata da iyalan su kan wannan biyan kudin hutun.
Ma’aikata a jihar Jigawa suna ta mika Godiyar su ga Maigirma Gwamnan jihar Jigawa kan wannan kulawa da ya basu. Mun kalli hakan a matsayin soyayya da tausawa inji ma’aikatan jihar.