LABARIN ALI NUHU DA JARUMA SHRADDHA ABIN KUNYA KO TOZARCI?
Daga Madina Ibrahim
Wata jarumar kasar Indiya ta fina-finan Bollywood ta kunyata fitaccen jarumi Ali Nuhu
Hakan ya biyo bayan kin kula shi da ta yi a shafinta na Instagram bayan ya wallafa hotonta yana yi mata murnar ranar haihuwa
A ranar 17 ga wannan watan ne jarumar take cika shekaru 31 a duniya, inda kuma take yin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa na Kannywood, Ali Nuhu, ya sha kunya bayan jarumar fim ta kasar Indiya ta share shi taki yi masa magana bayan yayi mata magana.
Dabo FM ta bankado cewa fitacciyar jaruma, Shraddha Arya, taki kula jarumi Ali Nuhu ne bayan ya aika mata da sakon taya ta murnar ranar zagayowar haihuwarta.
Jaruma Shraddha Arya, da ta cika shekaru talatin da daya (31) da haihuwa, tana gabatar da bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta a duk ranar 17 ga watan Agusta na kowacce shekara.
Jarumi Ali Nuhu dai ya wallafa sakon ne a ranar 17 ga watan Agustan wannan shekarar a kan shafinsa na Instagram.
Inda har ya zuwa yanzu da muke bada wannan rahoto jarumar ba ta ce masa uffan ba akan hoton nata da ya wallafa.
An gano cewa ya zuwa yanzu jaruma Shraddha Arya ta wallafa sakonnin mutane sittin da daya a shafinta na Instagram wadanda suka taya ta murnar, amma babu Ali Nuhu a ciki. Wanan ya sanya wasu ke ganin cewa jarumar ta kunyatashine ko kuma ta tozartashi?