KU KARANTA – BUHARI BAI TABA ZUWA MAKARANTA BA TAKARDUN BUGE YAKE AMFANI DASU- BUBA GALADIMA

KU KARANTA – BUHARI BAI TABA ZUWA MAKARANTA BA TAKARDUN BUGE YAKE AMFANI DASU

Inji Buba Galadima

Aliyu Mustapha

Tsohon na hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shugaban kasar bai taba zuwa makaranta ba a rayuwarsa

Bayan haka kuma Buba Galadima ya bayyana cewa duka takardun da shugaban kasar ya ce yana da su na bogi ne
Sannan kuma ya bayyana cewa shugaban yana kokarin tilasta alkalai su bashi nasara a kotu kan shari’ar zabe da ake yi

Tsohon na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba zuwa makaranta ba a rayuwarsa kuma duk takardun da yace yana da su na bogi ne.

Wannan magana dai ta fito daga bakin Buba Galadima ne, wanda ya kai ziyara gidan talabijin na Channels TV, sannan kuma ya bayyana cewa shugaban kasar yana tsoratar da alkalai da masu shari’a domin su saka ya samu nasara a kotu akan shari’ar zabe da ake yi a yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *