Zamu hada kai da kamfani domin tura yaran talakawa karatu a kasar waje
Gwamna A.A.Sule
Daga Zubairu M Lawal
Gwamnan yace zamu hada giwa da wata kamfani mai zaman kanta ta harkan rarraba wutan lantarki ( Oriental Energy Resources) dumin duba Dalubai masu hazaqa suje karatu a kasashen wajen.
Yace ; dalubanmu dake karatu zamu qarfafa masu giwa masamman wadanda basu da galihu zamu basu tallafin zuwa karatu a qasashen.
Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya bayyana hakane wajen
rabawa matasa injunan ginin Jan Bulo ta zamani injunan da daruruwan matasa ne zasu amfana dashi wajen ayyukan dogaro da kai.
Da yake jawabi Gwamna Abdullahi Sule yace; samar ga ayyukan yi ga matasa yana cikin qudurin wanan Gwamnatin.
Babban burinmu shine mu inganta rayuwar matasa ta hanyar samar masu da ayyukan yi da zai kawar da zaman banza.
Wannan injunan na ginin Bulo ta zamani an koyarwa wadanda zasuyi amfani dashi ne kafin a rabashi Ayau.
Matasa maza da mata da yawansu yakai 200 zasu iya yin aiki da injunan guda arba’in da daya.
Wannan mun soma kenan akwai matakai dabam dabam da mukeson kaiwa domin taimakawa rayuwar matasanmu.
Akwai halaqa ko hadin giwa domin samar da wasu hanyoyin taimakawa alumman jihar Nasarawa tsakanin mu da Babban Bankin Nijeriya.
Makarantar koyan qere- qeren zamani da muke dasu zamuyin kokari mu bunqasasu. Domin samar da Sana’a qere – qere ga Matasanmu masamman wadanda ke makarantun.
Yanzu lokaci ya wuce da za’ace zuriyar Gwamna Abdullahi Sule ne ko na Mataimakin Gwamnan Emmanuel Akabe sune zasu amfana domin cin gajiyar dukiyar jihar Nasarawa.
Yace; duk yan jihar Nasarawa suna da kaso cikin abinda ake kawowa burinmu kowa ya amfana da abinda ake samu.
Da yake zantawa da Wakilinmu Hon. Kwante Yakubu mai taimakawa Gwamna a vangaren wasanni da harkokin matasa. Yace; wannan tallafin da Gwamna Abdullahi Sule yabada ba wani sabon abu bane .saboda lokacin da aka rantsar dashi yayi alkawarin taimakawa matasa da kayan Sana’a kamar inujuna saqa da injunan niqa Kuma ya cika alkawarin.
Babu abinda zamu cewa Gwamna saboda ya riqe harkokin tallafawa matasa . kuma muna saran nan da wani lokaci qanqani matasan jihar Nasarawa zasu kunnu doki da na wasu manyan jihohin da sukaci gaba.
Sanna Kwanta Yakubu yayi kira ga matasa dasu daina ta’amali da miyagun kwayoyi su natsu guri daya su taimakawa kawunansu ta vangaren Ilumi .