GOBARA DAGA TEKU MUTUM 8 SUN MUTU
Daga Zubairu M Lawal
An tabbatar da mutuwar mutane takwas a lokacin da wani jirgin ruwa na shata ko haya ya kama da wuta a yankin gabar tekun kudancin California, a Los Angeles da ke Amurka.
Masu tsaron gabar tekun Amurka sun ce an gano gawarwakin mutum hudu, da kuma wasu karin hudu a karkashin tekun, a kusa da inda jirgin yake. Amma kuma har yanzu ba a gano wasu 26 ba, yayin da ake ci gaba da aikin ceton.
An dai kunna kuwwar neman taimako ta jirgin ruwan a lokacin da wutar ta kama da misalin karfe 3:30 na dare agogon can, wadda jinta ke da wuya, sai jami’an tsaron gabar tekun suka tafi kai dauki jirgin wanda a lokacin wuta ta mamaye shi.
Kafin isarsu wurin, jiragen ruwa na daidaikun jama’a wadanda suka fara isa wurin, sun yi kokarin ceto biyar daga cikin ma’aikatan jirgin, wadanda a lokacin da wutar ta tashi daman su ba barci suke ba.
Masu linkaya ne dai a jirgin ruwan na shata mai tsawon mita 22 mai suna Conception. Yankin tekun da abin ya faru da ake kira Chanel Islands, yawanci daman masu wasan linkaya ne da kamun kifi suka fiye zuwa wurin.
Ba a dai san abin da ya haddasa gobarar a jirgin ruwan ba zuwa yanzu, amma wasu rahotanni na cewa an ji karar fashewar wani abu kafin wutar ta tashi.
Jirgin dai yana wurin da ke da tazarar mita 20 ne daga bakin gabar tekun tsibirin Santa Cruz, abin da ya sa ake kyautata fatan cewa wasu daga cikin mutanen cikin jirgin kila sun yi iyo suka tsira.
Jami’an tsaron bakin tekun sun ce ana ci gaba da aikin kokarin ceton, amma kuma ga yadda yanayi yake ana yanke kaunar sake gano wani da ke da sauran numfashi.