Dubban yara sun amfana da aluran rigakafi. Shan-inna
Daga Zubairu T M Lawal Lafia
Dubban yara qanan yan qasa da sheakaru uku sunfi amfana da shirin aluran rigakafin cutar shan-inna da aka gabatar a wasu jihohi a fadin Nijeriya.
Da yake zantawa da manema labarai a taron bita bayan gabatar da Shirin Foloyin Dakta Faisal Shauaibu yace; alumman Nijeriya sun ansa wanan shirin hannu biyu biyu .
Yace; yara yan qasa da shekaru uku maza da mata aka yiwa aluran a ko ina .
Ya qara da cewa kungiyoyin da suka taka mahimmiyar rawa wajen ganin an kawo qarshen cutar shan-inna a nahiyar Afirika sun hada da kungiyar kiwon lafiya ta Duniya.
Da kuma kungiyar kula da qananan yara ta Majalisar Xinkin Duniya UNICEF dama kungiyar CDC daga qasar Gamaniy.
Yace; babban fatanmu shine moga kafin shekarar 2020 mu tabbatar an samu raguwar cutar shan-inna dama na Bakon-doro da kashi 90% .
Da yake magana Dakta Peter Clement yace; yadda muke samun hadin kan Gwamnatochin jihohi a wanan lamarin yana tabbatar da samu. Nasarar kawar da cutar shan-inna.
Yace; yanzu kowata Gwamnati burinsu tabbatar da samun lafiyan alumma. Ya kuma ce ;suma iyayen yara suna taka rawa sosai wajen kawo yaransu masamman a qananun Asibitochi na sha-katafi dake yankunansu ko a gundumominsu.
Yace; a wanan karon an samu cigaba sosai wajen fahintar da alumma illolin cutar.
Ya qara da cewa; a shekarar 2016 mutani basu fito da yara sosai kamar yadda a wanan shekarar suka fito dasu ba.
Yace; Gwamnatin tarayyan Nijeriya tana qara himma wajen ganin an kawar da cutar shan-inna a fadin qasar baki daya , sabanin qasar da yanzu sukafi fama da barazanar cutar kamar Pakinstan da Afganinstan