Yadda mutani zasu kare kansu daga hadarin cutar HIV
Daga Zubairu T M Lawal Lafia
Majalisar Xinkin Duniya ta koyar da malaman hanyoyin da zasu kare masu fama da cutar HIV wato (kanjamau).
A wanani taron bita da Majalisar Xinkin Duniya ta gabatar ga Ma’aikatan kungiyar Majalisar Xinkin Duniya dake kula da yara qanana.
Da shekarunsu bai zaice ishirin ba. Da yake zantawa da tawagar Ma’aikatan Mister Edward Kallon. Yace; Majalisar Xinkin Duniya ta himmatu wajen wayar dakan alumma ta yadda zasu kare kansu daga hadarin cutar qanjamau.
Yace; cutar qanjamau cutace da take da hadari ga wanda baya ba da kulawa wajen shan magani.
Yace; sau da yawa wadanda suka kamu da cutar suna daurawa kansu damuwa na ganin sun kusa mutuwa.
Yace; lamarin ba haka yake ba . mutum baya mutuwa sai kwananshi ya qare. Amma yana da gayar mahimmanci ga mai cutar qanjamau su kusanci san magani da ake basu.
Yace; matukar wanda ya kamu da cutar idan ya garza zuwa Asibiti ya karbi magani, kuma aka maida hankali wajen shan magani to mai cutar zasu zama tankar babu cuta a jikinsu.
Ya qara da cewa cutar qanjamau bata hana wanda yake da cutar cin wani irin abinchi. Ko wani irin abinchi mai cutar yaga damarci zai ci. Kuma zai iya shan komai babban buqatar da ake so mai cutar ya kula shine san magani.
Cutar bata da bara zana ga wanda ya kamu da ita na miji ko mace matukar za’a kula da shan magani.
Yace; hanyoyin kamuwa da cutar sunanan dayawa kama daga wajen jima’i zuwa amfani da abubuwa masu kaifi da zai janyo zub da jini kamar reza ko wuqa da alura da mislla, da sauransu.