Sarkin musulmi ya yi kira a kan ilimin mata da kananan yara.
Daga Zubairu M Lawal
Sarkin Alhaji Sa’adu Abubakar ya yi kira akan a kara mai da hankali akan karatun mata da kananan yara. Sannnan kum ya yi kira akan a kara mai da hankali wajen kula da lafiyar su.
Sarkin ya fadi wannan maganar ne a lokacin da wasu daga cikin jami’an majalisar din kin Duniya da suka kamu masa ziyara a fadarsa a birnin Sokkwato a karkashin jagorancin shugaban masu tsare-tsare na majalisar Dinkin Duniya Mistake Edward Kallon.
Sarkin Musulmin ya roki Majalisar Dinkin Duniya data miqetsye wajen ganin yaran mata da qananan yara sun samu ilumin zamani saboda zai amfani rayuwarsu sosai.
Sarkin ya koka da yadda rayuwar mata da qananan yara yake gararanba yanzu a qasan nan.
Yace; rashin baiwa ya’ya mata ilumi ba qaramin lilla bace ga qasa saboda idan basusan mahimmanci ilumi ba koda sunyi aure sun haifi yara yaran suma haka zasu taso ba tare da kulawa da basu ilumi mai inganci ba bare tarbiya.
Ya qara da cewa ilumin yara mata tankar gina alumman qasa ce.saboda zata tarbiyantar da yara ta kula da zaman takewar iyalanta.
Shima a nasa jawabin Jagoran tafiyar ta Majalisar Dinkin Duniya Mista Edward Kallon , yayi kira ga Shugabannin alumma wato Sarakuna dasu qara qaimi wajen kiraga alumma domin samun dawamammiyar zaman lafiya.
Yace; hakiqa zantukar da Mai martaba Sarkin Musulmi ya fadi zantukane da suke da mahimmanci saboda baiwa mata ilumi gina alumma ne.
Yace; yadda yanzu Duniya tafada cikin wani hali na rashin tsaro mata suna da rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya . to amma sai da ilumi mace zata taka rawar .
Sanan ya qara jan hankali ga mahukunta dasu riqa damawa da mata da sukayi karatu a cikin harkokin Gwamnati saboda zaibaiwa na baya kwarin giwa suma suyi karatu domin samun aiki a Gwamnatance.
Yace; yanzu Majalisar Dinkin Duniya ta dukufa wajen wayar da kan mata da fadakar dasu mahimmanci ilumi. Sanan takan dauko masu hazaqa domin basu muqamai suyi aiki kafada da kafada.
Yace; yanzu a zuren Majalisar Dinkin Duniya akwai mata da dama masu riqe da manyan muqamai.
Ita ma Iran a nata bangaren tana kokarin ta yayyafa wa wutar da ke ta ruruwa ruwa, ta rage zaman tankiyar da ke karuwa.
A ranar Talata, Shugaba Hassan Rouhani na Iran din a wurin babban taron Majalisar Dinkin Duniya, ya gabatar da shawarar samar da wani sabon shirin tsaro a kasashen yankin Fasha.
Sai dai karamin ministan na Saudiyya kuma, Al Jubeir ya yi watsi da shawarar yana mai bayyana ta da tamkar bai wa kura ajiyar nama ne.