ALI NUHU YA SAMU KYAUTA A TARON CITY PEOPLE NA SHEKARA

ALI NUHU YA SAMU KYAUTA A TARON CITY PEOPLE NA SHEKARA

Daga Ibrahim Lawal

Shahrarren jarumin fina-finan Kannywood da Nollywood, Ali Muhammad Nuhu, ya yanki tutar gwarzon diraktan shekara a taron ba da lambar yabon City People Entertainment Awards na wannan shekaran.

Taron lambar yabon na aukuwa ne a kowani shekarar karkashin jagorancin mujallar City People ga jaruman Najeriya da Ghana.

Ali Nuhu jarumi ne kuma dirakta ne a fina-finan Kannywood da Nollywood.

Sauran wadanda suka samu lambar sun hada da Hafsat Idris, wacce ta ci taurariyar shekara; sai Abubakar Maishadda wanda yaci frodusan shekara da fin din da ya hada ‘Hauwa Kulu’.

Sauran Misbahi Anfara da Hassana Muhammad.
An gudanar da taron ne ranar Lahadi, 13 ga watan Oktoba, 2019 a jihar Legas.

A wani labarin duk da mafi yawan sassan Najeriya basa samun hasken wutar lantarki, gwamnatin tarayya ta kashe fiye da tiriliyan N4.7 a bangaren wutar lantarki daga shekarar 1999 zuwa 2010.

Shekaru takwas bayan hakan, gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, da gwamnati mai ci ta shugaba Buhari, sun kara kashe karin tiriliyan N1.164 a bangaren wutar lantarki, amma har yanzu masana’antun cikin gida sun dogara ne da injina domin samun wutar lantarki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *