GWAMNATIN JIHAR NEJA NA BIYAN FANSHONOYA HAKOKINSU

GWAMNATIN JIHAR NEJA NA BIYAN FANSHONOYA HAKOKINSU
Daga Babangida Bisallah

Hukumar kula da biyan fanshon ma’aikatan Gwamnati a jihar Neja ta shiga rana ta uku dan tantance tsoffin ma’aikatan da su ka yi ritaya tare da bayansu hakkokansu.

Hukumar wadda ta raba aikinta a zangon uku na yankunan Neja ta tsakiya, Arewa da Kudu. Wanda aka fara aikin littinin din makon nan, inda aka fara da Zone ‘A’, Neja ta Kudu. Inda a yau kuma za a shiga Zone ‘B’, Neja ta tsakiya wanda da zaran an kammala za a shiga Zone ‘C’, Neja ta Arewa.

Hukumar tayi kiran dukkanin tsoffin ma’aikata da suka yi ritayar aiki daga yankunan kananan hukumomi da su ziyarci sakatariyar hukumar dan bincikar sunayensu ta yadda za su samu kudaden su kamar yadda doka ta tanada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *