GWAMNATIN NEJA NA BIYAN ZUNZURUTUN BASHI DA PDP TA GADARWA JIHAR
Daga Babangida Bisallah
An bayyana cewar rashin ayyukan raya kasa da jam’iyyar PDP ta zargin Gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello na jam’iyyar APC da yi, ya biyo bayan halin da Gwamnatin PDP ta janyo wa jihar tsawon shekaru sha shida na mulkinta.
Jigo a jam’iyyar APC ne Alhaji Awaisu Wanna ya bayyana hakan ga manema labaru a minna.
Awaisu Wanna yace kowani wata tun bayan hawar Gwamnatin nan kan mulki ta ke biyan bashin da Gwamnatin PDP ta gadar mata, domin tun bayan zuwanta ta ke biyan naira miliyan dari shida a bashin da ba ita ta ciwo ba, domin da farko bankunan da aka ciwo bashin sun ce lallai ne gwamnati ta rika biyan naira miliyan dari takwas,
duba da in biya wadannan kudaden yasa dole aka tsaya akan naira miliyan dari shida wanda idan aka hada wadannan kudaden sai sun kai sama da biliyan bakwai a shekara, to ta ya Gwamnati za ta iya yin aikin bayan an barta da mugun miki.
Alhaji Awaisu ya jawo hankalin jama’ar jiha da cewar su yi watsi da surutan PDP rashin mafadi ne kawai ke damun su, wanda nan bada jimawa ba Gwamnatin jiha za ta dau matakai akan wadannan kudaden da ta ke biya alhalin ba san abinda aka yiwa jihar da su ba.