JARUMAN HAUSA FM TANA ZAMAN BAKWANTA A GIDAN KURKUKU
Daga Madina Ibrahim
Wata kotun majistare mai zama a Kano ta bada umarnin cigaba da tsare Fitaciyyar tsohuwar jarumar
Kannywood, Sadiya Haruna
Idan bamu manta ba furodusa Isa A. Isa ne ya maka ta gaban kotu sakamakon zargin ta da bata masa suna.
Jarumar ta fito kafafen sada zumunta ta sanar cewa sunyi auren mutu’a da furodusan tare kuma da kiransa da mummunar kalma na cewa dan
luwadi.
An gurfanar da wacce ake zargin ne akan laifin bacin suna wanda yaci karo da sashi ma 391 na Penal Code kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Sai dai wanda ake tuhumar ta musanta laifinta tare da kuma kin amincewa da laifin da aka karanto mata.
Lauyan wacce ake zargi, Y. A Sharif ya bukaci kotun da ta bada belinta amma dan sandan mai gabatar da kara, Jacob Yaduma, ya soki bukatar belin.
Yaduma yace; wacce ake zargin zata iya tsallake belin ko kuma lalata binciken da ‘yan sanda ke yi bayan belin.
Mai shari’a, Jastis Muntari Dandago, ya dage shari’ar har zuwa ranar Juma’a, 18 ga watan Oktoba, 2019.
Alkalin ya bada umarnin cigaba da tsare jarumar a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a dubi bukatar belin nata.