KIMANIN YARA MILIYON DAYA SUN KOMA MAKARANTA A BORNO

Kimanin yara miliyon daya sun samu damar komawa makaranta

Daga Zubairu M Lawal

Kididigar alkalumar Hukumar kula da yara qanan ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta tabbatar da komawar yara Qanan kimanin miliyoyin daya  zuwa makarantun Boko a yankin jihar Barno dake Arewa maso gabashin Nijeriya .

Da yake jawabi wajen bikin murnar komawar Dalubai makarantun su Mista Peter Hawking wakilin Hukumar kula da yara kanana ta UNICEF a Nijeriya .

Yace; abin farin cikine a garemu da iyayen yara da mukaga yara sun koma makarantun su domin samo ilumi mai inganci da zai taimakawa rayuwarsu.

Akasarin Dalubai suna karatune a yankunan bayan gari na Maiduguri wanda suka rasa karatunsu sakamakon rigingimun Boko haram.

Zasu samu ilumi mai inganci a wanan karon sakamakon hadinkai da Hukumar UNICEF tare da Hukumar Ilumin bai daya ta jihar Barno .

Hukumar kula da ilumin bai daya ta jihar Barno ta samar da makarantun piramare birni da karkara wanda Dalubai zasu samu damar gudanar da karatu ba tare da tangarda ba.

A nasa jawabin Gwamnan jihar Barno Farfesa. Babagana Zulum ya yabawa Hukumar kula da yara kananan ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF dagane da rawar da ta taka wajen ganin yara sun amfana da harkan ilumi.

Yace;Gwamnatin jihar Barno tayi farin cikin hada hannu da UNICEF wajen tallafawa rayuwar yaran jihar.

Farfesa Zulum wanda ya samu wakilcin Mataimakin Gwamnan  Alhaji Umar Usman Kadafur, a wajen taron.yace taron wayar dakan iyayen yaran ba zai tsaya a nan gurin taron bane kadai.

Gwamnatin jihar zata fadada shirin domin wayar dakan iyaye kuma zatayi amfani da Shugabannin alumma mazauna karkara su tsaya tsayin daga wajen ganin yara sun tafi makaranta.

Yace; Gwamnatin jihar Barno ta tanadar da kayan karatu da abinchin Dalubai dama abubuwan more rayuwa domin yaranmu.

Yace; Gwamnatin ta tattaro dubbannin yaran dake rayuwa a sansanoni yan gudun hijira da yaran almajirai kimanin
115,000, da samar masu da komai na karatu domin su samu ilumi.

Yace; a yanzu babu abinda Gwamnatin jihar Barno zatayiwa wadanan yaran face ta kula da karatunsu da matsalolin su na yau da kullun saboda su zama Shugabannin gobe.

Shima Farfesa . Bulama Kagu cikin jawabinsa ya tabo yadda rayuwar yara ya shiga cikin kunci a yankin Maiduguri.

Yace; Amma yanzu Gwamnatice uwarsu itace Ubanshu kuma zata kula da tarbiyarsu da iluminsu. Ya qara da cewa iyaye da masu fada aji su sanya ido akan rayuwa yaran su kula da karatunsu saboda Gwamnati tayi rawar gani wajen dauke masu abubuwan da zai dame rayuwarsu kamar yunwa da matsalar sutura.

To babu abinda ya rage garesu face suyi karatu saboda karatu shine abinda zai amfanesu nan gaba su zama Shugabannin na gari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *