NAYI TIR DA ALLAH WADAI DA MUSULMAI – MERKEL

Na Yi Tir Da Allah Wadai Da Musulmi Inji – Merkel

Daga Aliyu Mustapha

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fito fili ta soki lamirin al’ummar musulmi, bisa ga abin da ta kira saƙa da mugun zare da su keyi a tsakanin su da kuma zaman su koma baya ga dangi idan aka kwatanta su da sauran jama’ar duniya.
Merkel ta yi wannan furucin ne a wata tattaunawa da ita da gidan talabijin na CNN ya yi, dangane da rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa na yankin gabas ta tsakiya.
Shugabar Jamus ɗin ta cigaba da cewar, abin mamaki ya ƙare akan musulmi, a matsayin su na masu bautar Allah ɗaya, da Annabin su guda ɗaya, hakazalika Littafin su ɗaya ne, amma duk da haka zaka samu suna kisan juna da zubar da jinin ‘yan uwansu wanda ko dabbobi ba sa aikata haka.
Angela Merkel ta cigaba da cewar, a duniyar Musulmi ne kawai za ka samu mai yin kisa yana faɗin Allahu Akbar, hakanan wanda ake kashewa shima yana faɗin Allahu Akbar.
Merkel ta bada misali da ƙasashen Sin da Hindu, inda ake da ɓangarorin addinai da dama sama da 150, amma duk da haka zaka samu suna zaune da juna lafiya saɓanin Musulmi masu abin bautawa guda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *