Shirin raya karkara da biranai Gwamnatin ta hada hannu dawasu kungiyoyin
Daga Zubairu M Lawal
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta hada giwa da wata kungiya mai samar da muradin cigaban raya karkara da biranai yarjejeniyar da aka kullashi a birnin New York.
Kungiyar cigaban raya qasashe da bunqasa alumma sun hada hannu da Gwamnatin Tarayya domin bunqasa yan kunan karkara da biranai a tarayyar Nijeriya .
Gwamnatin Tarayya ta aminche da wanan kuddurin ne a taron da aka gabatar a watan da ya gabata a birnin New York ta qasar Amurka tare da Shugaban qasar Nijeriya Muhammad Buhari da kuma Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi.
Kungiyar ta SDG da UNDP zasu dukufa wajen samar da ingantatun abubuwan more rayuwa ga alumman Nijeriya masamman mazauna karkara.
Haka zalika akwai amincewar kungiyar cigaban bankin Afirika wanda zasu hada karfi da karfe wajen ganin an samu ingantaciyar cigaba.
Ministan harkokin qasashen waje na Nijeriya Dakta Akinwunimi Adesina ya kasance a tsakani lokacin kulla wanan yarjejeniyar.
Tare da maibada shawara ta masamman a Majalisar Xinkin Duniya vangaren kungiyoyin raya qasashe Mista Geoffrey Onyeama. Dama babban Kodineta na Majalisar Xinkin Duniya dake Nijeriya Mista Edward Kallon a yayin taron.
Edward Kallon yayi fatan samun ingantaciyar cigaba a yayin gudanar da wanan aikin.
Yace zai samar da cigaban rayuwar alumman Nijeriya masamman marasa galihu dake rayuwa cikin matsanancin hali , a wasu kauyuka.
Haka zalika jagororin da suka halarci taron kamar Mista Muhamed Yahya wanda ya wakilci Mista Ojijo
Odiambo; da Chairman na Gwamnonin Nijeriya kuma Gwamnan jihar Ekiti Kayode
Fayemi; da ministan Kudi da kasafi Hajiya Zainab Ahmad da sauransu