DA GASKENE ADAMU ZANGO YAFI WASU GWAMNONIN AREWA AMFANI ?
Daga Aliyu Mustapha
Shugaban makarantar Professor Ango Abdullahi da ke birnin Zariya, Dr Shamsuddeen Aliyu Maiyasin, Garkuwar makarantar Zazzau, ya ce babu tantama kan naira miliyan 46 da fitaccen dan wasan Hausan nan, Adam Zango ya zuba a makarantar domin tallafa wa marayu 101 su yi karatu.
Dr Shamsuddeen ya kara da cewa ba wannan ne karon farko ba da fitaccen jarumin yake bayar da irin wannan gudunmawa ba ga marasa karfi musamman kan abin da ya shafi karatunsu.
A ranar Laraba ne dai Adam Zango ya wallafa batun tare da rasitin biyan kudin a shafinsa na Instagram.
Wannan batu ne dai ya janyo mahawara a kafafen sada zumunta, inda da dama ke ganin Adam Zango ba shi da kudin da zai iya biya wa marayu 101 kudin makaranta na shekara uku.
Jama’a da dama sun yaba da irin tallafin da Dan wasan ya baiwa marayu kuma sun gwarzanta bajintarsa.
Wasu sun bayyana shi a matsayin wanda yafi wasu Gwamnonin Arewa kishin talakawa. A yayin da wasu ke ganin abinda yayi ko masu mulki basu iyayi ba.
To sai dai wasu na kusa da jarumin inda suka shaida cewa “yana da gidauniya da ke neman tallafin mutane musamman masu hannu da shuni.”