GWAMNATIN NASARAWA ZATA KARA BUNQASA ILUMIN NAQASSASU – YAKUBU LAMAI

Gwamnatin Nasarawa zata qara bunqasa ilumin Naqassasu

Yakubu Lamai

Daga Zubairu  Lawal

Babban jami’in kula da harkokin yada labarai da sadarwa na Gwamnan jihar Nasarawa Alhaji Yakubu Lamai ya furta haka a taron bita da ya gudana domin jin ra’ayin Naqassasu a Jihar Nasarawa.

Alhaji Yakubu Lamai yace; Gwamnatin jihar Nasarawa tayi zarra wajen bunqasa ilumin Naqassasu a fadin qasan nan .

Saboda a jihar Nasarawa akwai katafaren Makarantar da aka samar saboda Naqassasu ta kowani irin Naqasa.

Makaranta ne na zamani mai inganci kuma komai kyautane, baya ga wadanda suke karatu a manyan makarantar gaba da Sakondire.

Dan haka ya buqaci jin ta bakinsu sakamon wasu korafin dake biyowa baya . yace Gwamnati tana kan bakanta na inganta rayuwar Naqassasu da kulawa da ilumin su.

Ya zuwa yanzu Gwamnati na qara zakulo masu hazaqa da suka cancanci zuwa Jami’o’i da sauran manyan makarantun dake qasan tana turasu.

shirin ilimi kyauta ga Naqasassu dake karatu a duka manyan jami’oin dake  jihar Nasarawa ba zai yanke ba  saboda Gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule  ta qara hannu wajen qara yawan  dalibai nakasassu da a yanzu suke karatu a manyan makarantun Jihar, da qasa baki daya, inji Yakubu Lamai.

Duk da cewa Naqasassun sun koka da matsalolin da suke fuskanta a yanzu, cewa yanzu suna biyan kudin a wadannan makarantu.

Dalibai nakasassun sun sanar da haka ne a jawabinsu a wajen wani taron tattaunawa na musamman da ofishin daraktan tsare-tsare da harkokin yada labaran gwamnatin jihar ya shirya aka gudanar a jami’ar jihar dake garin Keffi hedikwatar karamar hukumar Keffi a jihar a karshen mako daya gabata.

A jawabin shugaban daliban jami’ar nakasassu Sunday Musa yayi korafi cewa har yanzu suna cigaba da biyan kudaden makaranta da sauran caje-caje a jami’ar duk da cewa Gwamnatin jihar ta ba da umurnin a daina karban kudaden makarantansu a wadannan jami’oi.

Ya bukaci Gwamna Abdullahi Sule da ya gaugauta sa baki a lamarin ya kuma tabbatar an maidowa  nakasassun kudaden makarantan da suka biya.

Ya qara da cewa yazuws  yanzu hukumar  gudanarwar jami’ar tana karban kudade batareda sanin gwamnati ba.

Ya cigaba da bayyana cewa “Babban kalubale da muke fuskanta a yanzu a makarantan nan kuma shine na rashin wadanda ke karban magana wato Interpreters a turance a mahimman kwasa-kwasan da muke karanta a jami’ar nan da sauransu.

Abin takaici ne idan akayi la’akari cewa a yanzu wasu daga cikinmu ne ke aikin interpreters da hakan kesa sau dayawa yawancinmu bama iya fahimtar abubuwa da ake koya mana.

Kuma dalibai makafi cikinmu sukan samu babban matsala wajen tafiya asusuwansu a yanzu.

Shiyasa muke kira ta musamman ga Gwamnan jihar  ya taimaka ya samar wa dalibai makafi abubuwan inganta karatunsu musamman bus wanda zai rika taimaka wajen zirga-zargansu a ciki da wajen jami’ar nan.”

Shima anasa bangaren daya daga cikin dalibai nakasassun mai suna Isma’il Abdul ya koka dangane da yadda acewarsa bincike ya nuna cewa cikin kashi 15 na nakasassu dake jihar kashi 7 na karatu amma kashi 2 ne kacal cikinsu ke samun aiki da Gwamnati.

Ya kara da cewa a yanzu nakasassu a jihar suna matukar fuskantar kuncin rayuwa kasancewa mafi yawansu ‘ya’yan marasa galihu ne saboda haka acewarsa akwai bukatar Gwamnati ta dauki matakai na share musu awaye musamman ta hanyar samar musu da aiki.

Tunfarko a jawabin mai taimakawa Gwamnan jihar Nasarawa akan harkokin nakasassu alhaji Musa Awe ya bayyana cewa a kokari da Gwamnatin jihar karkarshin jagorancin Abdullahi Sule keyi na inganta harkokin nakasassu a jihar tuni Gwamnan ya kafa wani kwamiti da zai bincika ya kuma gana matsaloli da suke fuskanta a makarantunsu dama wadanda basu samu damar karatu ba don tallafa musu a wannan bangare.

Anasa jawabin Shugaban jami’ar farfesa Suleiman Mohammed wanda yayi jawabi ta bakin mataimakinsa a fannin ilimi wato farfesa Peter Osuorji ya bayyana cewa hukumar gudanarwar jami’ar tana iya kokarinta wajen taimakawa nakasassun a fannin karatunsu inda acewarsa a kusan duka tsare-tsare da dokokinta takan yi la’akari da jindadinsu a jami’ar.

Ya kara da cewa akan haka nema yasa tuni mahukuntar makarantan ta umurci a rika samar wa nakasassu nasu dakin kwana na musamman da sauransu a gine-ginen wajen kwanciyar daliban jami’ar don yin la’akari da matsalolinsu.

Daganan sai ya bukaci dalibai nakasassu cewa kada suyi wata-wata wajen kai karar duk wani ko wata dake cin razafinsu akoyaushe ga mahukuntan jami’ar don karesu.

Taron tattaunawa da daliban jami’ar nakasassu ya samu halartar nakasassun da dama da malamansu da sauran shugabanni sashin karatu dabandaban a makarantan da jami’an gwamnati da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *