IDAN MUTANI ZASU DARAJA JUNANSU ZA’ASAMU ZAMAN LAFIYA A DUNIYA – MDD

Idan mutani zasu daraja junansu za’a samu zaman lafiya a Duniya

Antonio
Daga Zubairu  Lawal

Shugaban Majalisar Xinkin Duniya Mista Antonio Guterres� ya bayyana haka a sakon ranar Biranai ta Duniya. Sakatare Janar na Majalisar Xinkin Duniya yace; kowani mutum yanada daraja kuma yana da rawar da zai iya takawa wanda alumma zasu amfana.

Saboda haka wajebine mu mutumta junanmu mu yarda dukkaninmu mutanine kowa da darajarsa. Idan muka daraja junanmu babu wariyar launin fata ko bambamcin qabila dana addini sai a samu zaman lafiya.

Majalisar Dinkin Duniya ta zabi ranar 31 ga watan Oktoba a matsayin Ranar Birane ta Duniya.

An yanke wannan hukuncin ne dai domin   abun kasa rayuwar Al’umar da suke zama a cikin Birane, dan ya zama rayuwar su ta tafi da irin yanayin da ya kamata Biranen su zama.
A taron dai na 2019 wanda aka ba take ‘canja Duniya domin mutane masu zuwa su more rayuwa’, an fito da wasu matsaloli wanda mazauna birane ke fama da shi, da kuma hanyoyin da ya kamata a warware su.

Masu shirya taron dai sun ce duk shekara za’a rinka ba taron ta ke da yanayin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *