SHUGABAN YAN JARIDA YA ZAMA KWAMISHINA A NASARAWA

Shugaban yan jarida ya zama kwamishinan yada labarai a Nasarawa

Daga Zubairu .Lawal

A ranar jumaa 1/11/2019  ne Gwamna Abdullahi Sule ya cika wata biyar bias karagar Mulkin jihar Nasarawa kuma a ranar ne ya rantsar da sabbin {wamishinonin da zasu taimaka masa wajen tafiyar da harkokin Gwamnati.

Cikin kwamishinoni goma sha biyar da Gwamnan ya nada Shugaban yan Jarida na jihar Nasarawa {wamared Dogo Shama ya samu kasancewa a cikinsu.

Da yake jawabi ga sabbin {wamishinonin Gwamna Abdullahi Sule ya ummurcesu dasu bada himma wajen samar da cigaban jihar Nasarawa masamman ta hanyoyin samar da kudaden shiga sakamakon jihar tana cikin hadarin rashin wadacecen kudaden da zata tafiyar da ayyukan cigaba.

Gwamnan yace wadanda aka rantsar a matsayin {wamishinonin hazikan mutanine da zasu kai jihar Nasarawa zuwa ga tudumna tsira. Shi yasama da aka tura sunayensu gaban majalisar jihar yan majalisar Dokoki na jihar basu bata lokaci ba wajen tantancesu.

Gwamnan ya bu{aci {wamishinonin das u zage dantse wajen kirkirar sabbin hanyoyin ayyukanyi ga alumman jihar wanda alumma zasu karu kuma jihar ta amfana da kudaden shiga.

Gwamnan yace yanzu haka akwai hanyoyi da muke bukatar kamallasu nan bad a jumawaba akwai hanyoyi a cikin garin Lafia dama sauran {ananan hukumomi da suke bukatar samun cigaban.

Sannan akwaishirin sanya wutan lantarki na kan hanya a dukkanin kananan hukumomin dake fadin jihar. Da kuma batun bunkasa ayyukan gona saboda wqannan jihar tana cikin jerin jihohin da ake tinkaho dasu wajen manoma.

Akwai shirin samar da katafaren gonan shinkafa na kamfanin Dangote dama sauransu, saboda haka bazamuyi wasabi zamu dukufa wajen bada fifiko a harkan noma.

Haka zalika batun tsaro Gwamnati ta kara dammara wajen tabbatar da samun zaman lafiya mai dorewa cikin jihar  Nasarawa kuma tana bukatar alumman jihar dasu bada hadin kai wajen tabbatar da zaman lafiya.

Bayan rantsar da {wamishinoni goma sha biyar an kuma rantsar da masu baiwa Gwamnati shawara su goma sha biyu da kuma Babban joji guda daya da Shugabannin hukumar jin dadin Alhazai na {asa reshen jihar Nasarawa dama hukumar jin dadin masu ziyara zuwa Jarusalam na {asa reshen jihar Nasarawa daga nan aka baiwa kowani {wamishina ofisin da zai gudanar da ayyuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *