KIMANIN MUTUM MILIYON 23 KE FAMA DA CUTAR HIV A DUNIYA -ANTONIO

Kimanin mutum miliyon 23 ke fama da cutar Kanjamau

Inji, Antonio

Daga Zubairu  M Lawal

Babban Sakataren Majalisar Xinkin Duniya Mista Antonio Guterres ya bayyana haka a sakon da ya aika na ranar tunawa da masu fama da cutar kanjama’u ta Duniya.

Mista Guterres yace; a kiddidigar da suke dashi a Duniya kimanin mutani miliyon 23 suke fama da wanan cutar.

Yace ; amma suna fatan nan da shekaru 2030 Duniya zatayi ban kwana da wanan cutar ta Kanjama’u.

Yace; cikin tsarin cigaban da hukumomin dake kula da wanan sashin na Majalisar Xinkin Duniya keyi suna kokarin samar da sinadarin maganin kawar da cutar a Duniya baki daya.

Ya qara da cewa; kawar da cutar HIV zai lashe zunzurutun kudi kimanin dalar Amurka biliyon daya. Kuma da zarar an tabbatar da hada sinadarin za’ayi amfani dashi kota ina a Duniya.

Za’a tabbatar da ya shiga birni da karkara,Kuma ayi amfani da Shugabannin alumma wajen yekuwar isar da wanan sakon.

Hakama kafafen yada labarai zasu taka mahimmiyar rawa wajen isar da sakon sinadarin ga alumman Duniya.

Mista Antonio Guterres yace; yana jin dadin yadda masu fama da cutar HIV suke kulawa wajen shan magani da yake taimaka masu wajen karesu daga rage karfin cutar.

Yace; cutar Kanjama’u baya hana mutum gudanar da ayyuka kuma baya hana mutum cin wasu nau’in abinchi , bukatarshi shine mai cutar ya kula da shan magani.

Saboda magani yana rage karfin cutar baya samu ya shiga wasu gurare a jikin mutum,sai dai yayi ta tsayuwa gu daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *