KO KUNSAN ME YASA – FASINJOJI TAFIYAR KILOMITA 100 A DAJIN ABUJA ZUWA KADUNA

Hamisu Abubakar

Rahotanni daga tsakiyar Dajin Abuja zuwa Kaduna sun tabbatar da cewar Jirgin kasa cike da Mutane ya mutu a tsakiyar Daji, ba gida gaba ba gida baya.

Rahotannin har ila yau sun bayyana cewar Jirgin kasan ya taso ne daga babban birnin tarayya Abuja zuwa Rigasa dake Jihar Kaduna garin Gwamna.

Zuwa yanzu babu ainihin dalilin lalacewar Jirgin, sai dai shedun gani da Ido sun tabbatar da shedar cewa Jirgin ya lalace a tsakiya Daji, karshe ma sai da Fasinja suka yi tafiyar kasa ta a kalla Kilomita 100 zuwa tashar Jirgin dake Rigasa.

Majiyarmu ta ruwaito cewar an yi kokarin taso wani Jirgin daga Abuja kan yazo ya karasa da su amma an yi hasashen Jirgin zai dauki Lokaci kafin ya zo, Fasinjojin sun sami rakiyar Jami’an tsaro zuwa tashar Jirgin.

Wakilin mu Shuaibu Abdullahi, yayi kokarin jin ta bakin masu ruwa da tsaki na Tashar Jirgin amma abun ya gagara har zuwa lokacin wallafa wannan Labarin.

KUNSAN ME YASA – FASINJOJI TAFIYAR KILOMITA 100 A DAJIN ABUJA ZUWA KADUNA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *