AN BUKACI A KARA TSARO A YANKIN AREWA MASO GABAS

An bukaci a kara tsaro a yankin Arewa maso gabas

Inji Amina Muhammad

Daga Zubairu M Lawal

Mataimakiyar Sakataren Majalisar Xinkin Duniya Hajiya Amina Muhammad tayi kiraga Gwamnatin Nijeriya data qara tsaurara matakan tsaro a yankin Arewa maso gabashin Nijeriya.

Mataimakiyar Sakataren ta bayyana hakane a wani taron masu ruwa da tsaki. Tace yan Ta’adda na qara yunkurin kawar da zaman lafiya da yake samuwa a Nijeriya.

Ya zama wajibi Hukumomi qasa dama na yankin Arewa maso gabas su kara yun kuri wajen kawar da yan Ta’addan domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Ta qara da cewa Gwamnatin Nijeriya tana amfana da tallafin Majalisar Xinkin Duniya masamman shirin da yan qasan kan samu na ayyukan cigaba ta mai dorewa.

Tace; Majalisar Xinkin Duniya tana koyar da sana’o’in hannu da ke taimakawa yan gudun hijira dake rayuwa cikin halin kunci a sansanonin .

Tace; sai Gwamnatin Nijeriya ta mike tsaye sannan wasu yankunan na Duniya zata sanya hannun taimaka mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *