Mata zasu iya gudanar da kowani irin aikin Gwamnati
inji Miminsta Pauline Tallen
Daga Zubairu M Lawal
Ministsn harkokin Mata da walwala Misis Pauline Tallen ta bayyana haka a lokacin da ake taron wayar da kan mata na Duniya .
Taron da ya hada kimanin mata da yawansu ya kai 1000 daga kungiyoyi dabam dabam a harabar cibiyar harkokin mata dake Abuja.
Tace; Mata suna da rawar takawa cikin kowata Gwamnati saboda mata suna karatu kuma suna tarbiyartar da yara kuma sunada rikon Amana. Tace; yanzu adadin kuri’un da ake samu na zave mafi yawa daga hannun mata yake fitowa.
Saboda mata Sune ke bada lokaci su zauna a layin zave kuma mata suna gudanar da yakin niman zave gida gida. Ta kara da cewa yanzu adadin mata dake tsayawa takarar kujerun siyasa yana dada karuwa ne a Nijeriya.
Ta yabawa Gwamnatin Shugaba Buhari cewa an baiwa mata manyan mukamai na siyasa.
Shima a nasa jawabin Farfaesa Tijjani Muhammad Bande ya shawarci kungiyoyin Mata da suka samu halartan taron dasu zama jakadun sauran matan da basu samu damar halartan taron ba.
Su sheda masu cewa lokaci ya wuce da mata zasu zauna a barsu a baya.
Yace; mata su mike tsaye saboda a rika damawa dasu wajen gudanar da ayyukan cigaba kansu da iyalansu da qasashensu.
Yace; idan mata suka samu damar rike mukamai a Gwamnati abubuwa sunafi cigaba.
Saboda mata suna da tausiyi kuma sune ginshikin cigaban kowata alumma. Yace; duk matakin da akeson a taka idan aka hada da mace za’akai wanan matakin cikin sauki.
Itama a nata jawabin wanda ta wakilce vangarorin Majalisar Xinkin Duniya Misis Comfort Lamptey, ta bukaci Gwa!natochi dasu rika ware kaso mai yawa na ayyukan Gwamnati su baiwa mata a Jihohinsu saboda mata suna da nauyi a kansu ga kula da yara qanana ga ayyukan gida da sauransu kuma suna kulawa da iyalansu fiye da yadda maza keyi.