SABON RIKICHI YA BARKE A APC SAI AN SAUKE OSHIMOHLE
Daga Hamisu Musa
Rikicin da ke faruwa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya dauki sabon salo mai cike da damuwa a ranar Talata, 14 ga watan Janairu, lokacin da mambobin kwamitin masu ruwa da tsaki suka yiwa yiwa Shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole tawaye a lokacin taronsu na farko.
Lamarin is ya fara ne a ranar Talata lokacin da daya daga cikin mambobin kwamitin masu ruwa da tsakin ya ce lallai bai kamata ya jagoranci taron jam’iyyar ba saboda jam’iyyar reshen jihar Edo ta dakatar dashi bisa ka’ida.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan fitowa daga taron, mataimakin Shugaban jam’iyyar na kasa (Arewa maso gabas), Mustapha Salihu, ya jingina dalilin rikice-rikicen kan tsayar da Waziri Bulama don cike matsayin babban sakataren jam’iyyar na kasa.
Ya yi barazanar jan shi zuwa gaban hukumar DSS , da sauran hukumomin tsaro idan ya ci gaba da jagorantar kowani zama ba tare da dage umurnin da ya dakatar dashi daga jam’iyyar ba.
Ya daura laifin dukkanin matsalolin da ke addabar jam’iyyar mai mulki kan tsohon gwamnan na Edo, cewa yana jagorantar jam’iyyar ta hanyar ajiye sunan Shugaba Buhari don tabbatar da ganin cewa duk wani hukunci ya yi daidai da son zuciyarsa.