MATA SUNA BADA GUDUMAWA A AIKIN JARIDA

MATA SUNA BADA GUDUMAWA A AIKIN JARIDA
Inji Shugaban NUJ

Daga Zubairu M Lawal

Ambaiwa yan jarida kyakyawar horo ta yadda zasu rika tantance labarai na gaskiya a yayin gudanar da aikin. Horor da aka gabatar da shi a wani taron qarawa juna sani a birnin Lagos ya samu halartan yan jaridu daga jihohi shida a fadin Nijeriya.

Kimanin yan jarida 33 ne suka samu nasarar halartan taron wadanda suka fito daga jihohin Lagos Abuja Ebonyi, Sokoto and Cross River da Adamawa.

Da yake cikin jawabin sa Shugaban kungiyar yan jarudu na jihar Lagos Mista Akinreti yace; yanzu ana kara samun cigaba cikin kungiyoyin yan jarudu saboda ana samun mata da dama suna shiga wanan aikin ana damawa dasu.

Yace; hazakar da mata suke badawa wajen aikin dauko labari yana kara kowa cigaba a fannin aikin jarida. Yace; a baya mata basu sha’awar aikin jarida saboda suna gani aikine mai matukar wahala.

Amma yanzu mata suna kafada da kafada da mazaje wajen gudanar da aikin, kuma na samun nasarori da cigaba.

Yace; duk abinda mata suka sanya kansu zasuyi to ana samu. Amfanu a ciki , yace ; yanzu mata da dama suna da kafofin yada labarai ta yanar gizo kuma suna rike manyan mukamai a gidajen jaridu .

Yadda mata suke gudanar da aikin ya kara samar da ayyukan yi ga dubban mata a Nijeriya . kuma suna kokari harma akanyi alfahari da su .

Shima a nasa jawabin Dakta Franca Attoh Malami a jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Lagos ya bayyana irin cigaba da ake samu a fannin yada labarai.

Yace; a bangaren koyon aikin jarida dake Jami’o’i yanzu mata sukanfi mazaje yawa a ajujuwa.

Dakta Jide Attah yayi kira ga yan jarida da su rika tabbatar da adalci wajen rubuta labari , su rika jin ta bakin kowata bangare saboda yana baiwa labarai armashi da inganci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *