IKON ALLAH : ALUMMA SUN GA HANNUN MUTUM YA BAYYANA A SARARIN SAMA

IKON ALLAH : ALUMMA SUN GA HANNUN MUTUM YA BAYYANA A SARARIN SAMA

Daga Zubairu M Lawal

daren ranar Alhamis 9 ga watan Janairun nan mutane da yawa suka ga wani hadari mai kama da hannun mutum ya bayyana a garuruwan Asuncion da Juazeirinho, dake yankin Paraiba Cariri na kasar Brazil.

Mutanen da yawa sun dauki hoton wannan ikon Allah, kafin hadarin ya washe.

Wadanda suka dauki hoton sun yi ta sanyawa a shafukan sada zumunta suna yin rubutu bisa fahimtarsu da wannan hannu.

Wani abin mamaki shine, an dauki tsawon lokaci hadari bai hadu ba a yankin kasar ta Brazil sai wannan rana da wannan hannu zai fito.

Mutanen yankin da yawa sun cika da mamaki akan wannan sabon al’amari. Wasu sun yi tunanin cewa wannan hannu, hannu ne na Allah.

“Ina fatan wannan hannu ba shine sanadiyyar faruwar wani mummunan al’amari ba a kanmu,” cewar wani mazaunin garin Asuncion.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *