GWAMNATIN NASARAWA ZATA DAUKI MATAKI KAN MASU KARYA DOKAR SHARA -KWAMISHINAN TSAFTAR MUHALLI

Gwamnatin Nasarawa zata dauki mataki kan tsaftar muhali

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Gwamnatin jihar Nasarawa zata dauki matakin ba sani ba sabo kan masu bijirewa dokar shara da ake gudanarwa duk karshen wata .

Da yake jawabi ga manema labarai Kwamishinan Ma’aikatan tsaftar muhalli da tsare – tsare na jihar Alhaji Musa Ibrahim.
Yace; Gwamnati ta tsayar da ranakun Asabar din qarshen wata a matsayin ranar tsaftar muhali. Amma abin bakin ciki sai ka tarar da wasu suna karya doka suna fitowa Sana’ar su , ba tare da sun gudanar da share gidajen su ba.

Yace; tsafa tana da mahimmanci ga rayuwar alumma saboda duk wasu cututuka ana saminsu ne daga kazanta.

Yanzu cututuka suna dadda  qaruwa ga cutar zazzabin cizon sauro ga na zazzabin Lasa wanda ake samu daga Bera da sauransu.

Idan mutani basu tsaftace muhallinsu mai zai hana sauro su addabi gidaje da dakuna nan kwana . Hakama Beraye zasu samu guraren yawo suna niman abinchi hanakan zai sanya su shigo inda ake ajiyar abinchi suna tsoma baki.

Ya qara da cewa ; Masu ababen hawa kamar yan kabo kabo da masu tukin moto su kasance masu kiyayewa subi doka
“Domin yanzu mun hada karfi da karfe da kowani vangare na jami’an tsaro dama Shugabannin alumma dana yan kasuwa da na Direbobi da na yan Achaba. Muna aiki tare duk wanda aka kama ya saba doka akwai kotun tafi da gidan ka da za a hukunta shi “.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *