MATSALAR TSARO : SANATA YA BUKACI BUHARI YA YI MURABUS
Daga wakilinmu
Shugaban Marasa Rinjiye na Majalisar Dattawa, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Murabus kawai, ya sauka,daga mulki ganin yadda matsalar tsaro ke kara kamari a kasar nan.
Ya yi wannan kira ne a ranar Laraba, lokacin da Majalisar Dattawa ke tattauna wani kudirin da aka nemi gabatarwa a kan kalubalen tsaro a fadin kasar nan, tare da bukatar a sauya tasarin tsaron kasar baki daya.
Abaribe, wanda shi ne wanda ya fara yin magana daga farko, ya dora laifin kasa magance matsalar tsaro kacokan a kan Buhari.
Sanatan ya nuna al’ajabin yadda Buhari ya ce ya na mamakin yadda matsalar tsaro ta kara kamari.
Daga nan kuma Abaribe ya ragargaji kakakin yada labaran Buhari, saboda ya kira Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) da lakabin jam’iyyar siyasa, don kawai ta yi tir da kashe-kashen Boko Haram.
“…Idan za ka tunkari batu, to ka tunkari batun tun daga tushe. Ba mu ne muka nada Sufeto Janar na ’Yan Sanda ba. Za mu je wurin shugaban kasa mu ce masa ya yi murabus kawai, ya sauka.” Haka Sanata Abaribe ya bayyana a zauren majalisa.
Daga nan sai Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya katse shi, ya ce masa gara ya maida hankali wajen magana kan matsalar tsaro kawai.
“ ‘Yan Najeriya sun zabi APC saboda alkawarin da ta yi musu cewa za ta magance matsalar tsaro a kasar nan. Amma ta fadi ba nauyi, ta kasa yin komai.
Sanata Abdullahi Adamu daga Jihar Nasarawa ya tashi ya caccaki Abaribe.
Abaribe sanata ne na PDP, kuma shi ne Shugaban Marasa Rinjaye, na Majalisar Dattawa.
.