BAYAN GANO MAI CUTAR LASA A NASARAWA GWAMNATIN JIHAR TA DAUKI MATAKI

Bayan gano cutar zazzabin Lasa a Nasarawa Gwamnatin jihar ta dauki mataki

Daga Zubairu  Lawal

Kwamishinan kiwon lafiya ta jihar Nasarawa Hon.Ahmad Baba Yaya ya bayyana wa manema Labarai cewa ya zuwa yanzu sun tabbatar da Mace daya wanda ta kamu da cutar zazzabin Lasa .

Yace ; lokacin da suka samu wanan labarin a dauki matan aka kaita babban Asibiti tare da wasu mutum hudu da aka samesu da zazzafar rashin lafiya kuma ake tunanin wanan cutar ne.

Bayan malaman kiwon lafiya sun gudanar da kwaje gwaje a tsakanin su ita kadai aka samun tana dauke da kwayar cutar ta Lasa.

Yace; ya zuwa yanzu Gwamnatin jihar Nasarawa ta kebe ta a Asibiti ana kuma bata kyakyawar kulawa ta yadda zata samu lafiya akan lokaci.

Kwamishinan yayi kira ga alumman jihar Nasarawa da su zamo masu kulawa da tsaftar muhali a ko da yaushe. Yayi kira ga iyayen yara da su rika kulawa da yaransu qanana .

Saboda yara suna shiga lungo sako kuma da zarar sunga abu sukan dauka su sanya shi a baki.

Ya qara da cewa akwai barazanar cututuka da dama ba zazzabin lasa ne kadai yake bara zana ga rayuwar alumma a yanzu ba.

Akwai cutar da ke shiga jikin mutani harma yayi masu illoli so sai. Akwai wanda yakan makantar da mutani dama wanda yake kawo kuturta da sauransu.

Yace; ana samun sauran cututuka ta hanyar ruwa mara tsafta da ta’amali da gurare mara tsafta.

Kwamishinan yace ; ya zuwa yanzu Gwamnatin jihar Nasarawa ta dauki mataki kariya ga alumman jihar ta hanyar wayar da kan alumma da kuma kiransu zuwa ga Asibitochi mafi kusa da zarar a fara bada maganin rigakafin cututuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *