RIKICI YA BARKE A LAGOS SAKAMAKON HANA SANA’AR ACHEBA
Wasu yan achaba da matukan Keke Napep da akafi sani da ‘a daidaita sahu’ sun gudanar da zanga-zanga a unguwar Ijora ta jihar Legas ranar Litinin kan dokar hana aikin babur da Keke Napep a jihar.
An samu labarin cewa an fara takaddama ne lokacin da yan sanda sukayi kokarin hana su zanga-zangar.
Yayinda suka kaddamar da zanga-zangar misalin karfe 8:21 na safe, yan babur da yan Keke Napep sun tare hanyoyi suna kona tayoyin mota.