Kafafen yada labarai na wayar da kan alumma a Duniya
Inji Edward Kallon
Daga Zubairu M Lawal Lafia
Babban jami’in harkokin yada labarai na Majalisar Xinkin Duniya mista Edward Kallon ya bayyana haka a bikin ranar kafar yada labarai ta redio.
Yace; Majalisar Xinkin Duniya ta ware wanan ranar ne da nufin girmama matsayi na rawar da gidajen radio suka takawa wajen fada kar da alumma.
Ya qara da cewa kafar yada labarai ta radio itace kan gaba wajen wayar da alumma. Saboda aka sarin mutani dake rayuwa a karkara suna samun mahimman sako da kafar yada labarai na gidan radio ne.
Hata mutanin da suke gona dama karkarar da basu mu’amala da wutan lantarki zaku tarar suna amfani da radio wajen jin halin da Duniya ke cika.
Ya qara da cewa ; mutani suna kara samun Ilumi da fahinta ta hanyar sauraron gidajen radio saboda shirye – shirye masu iluman tarwa da wayar da kai.
Shirye – shiryen da gidajen radio keyi ba wai ya kan tsaya a matsayin nishadi bane kawai akwai Ilumi mai zurfi a cikin sa .
Yace; Shugabannin Majalisar Xinkin Duniya sun nuna farin ciki da wanan ranar da aka ware domin masu sauraron gidajen radio.