ALLAH DAYA GARI BAM-BAM – YADDA AKA GUDANAR DA ZABEN SHARE FAGE NA NIMAN AURE A JIHAR BAUCHI

YADDA AKA GUDANAR DA ZABEN SHARE FAGE DA NUFIN NIMAN AURE A BAUCHI

Daga Zubairu Lawal

Yadda a makon da ya gabatane wasu matasa suka gudanar da zaben share fagen niman aure a tsakanin su . Matasan su biyu abokan junane ,kuma suna son Budurwa daya .

Nan suka bukaci ta bayyana wanda take so da aure a tsakanin su . Da hakan bai yuhu ba sai suka yanke shawarar tara alumma da nufin gudanar da zabe wanda yafi yawan kuri’a shine yayi nasara.

Lamari dai ya gudana ne a karamar hukumar Giade dake jihar Bauchi.

Budurwar mai suna Khadija tana makarantar Sakondire a aji uku.

Samarukan masu suna Inusa da Ibrahim suka amince da hakan, nan da nan suka shiga yakin neman zabe, (Campaign) kowa na zagayawa majalisoshin mutane tare da gidaje yana neman kuriarsu domin a zabeshi ranar zabe.

A karshe dai an fito filin zabe, inda manyan garin suka samar da kayan zabe tare da akwatunan jefe kuria tare da malaman zaben da zasu kula tare da kirga kuri’un da aka jefe….
Inusa shine wanda ya samu nasarar zama gwani a filin zabe, bayan kammala kirga kuri’un tare da lashe zaben da Inusa yayi, sai aka bashi Certificate na shaidar da zata bashi damar cigaba da zuwa zance wajen Khadija… domin ayu musu aure.

Sai dai abokin karawar tashi tuni ya garzaya zuwa kotun da aka tanadar domin korafi haka zalika ya garzaya zuwa gidan Hakimi inda ya nisanta kansa da wanan sakamakon zaben.

Cikin korafin tasa Ibrahim yace ; cikin wadanda suka kada kuri’ar akwai wadanda shekaru su bai kai ba . sanan an gudanar da zaben ne a kofar gidan abokin takarar tasa.

Saboda haka yake kalubalanyar sakamakon zaben

A ta bakin Khadija wanda aka gabatar da zaben a kanta tace ; ita fatanta Allah yasa haka shine mafi alheri .

Tuni dai wanda yayi nasarar ya shirya walima na tayashi murna .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *