GWAMNATIN NEJA TA SHA ALWASHIN SABUNTA TSARIN GINA JIHAR
Daga Awwal Umar Kontagora
Gwamnatin Neja bisa jagorancin gwamna, Alhaji Abubakar Sani Bello ta sha alwashin inganta tsarin jihar ta hanyar samar da dubarun bunqasa tattalin arzikin jihar da ya shafi dukkan qananan hukumomin ashirin da biyar da ke faxin jihar.
Babban sakatare a ofishin sakataren gwamnatin jiha, Alhaji Baba Wachiko Yahaya ne ya bayyana hakan a tarukan sauraren ra’ayoyin jama’a da hukumar samar da sabon tsarin birane na gwamnatin jihar ta shirya a sassa huxu da hukumar ta shirya a jihar, bisa jagorancin Farfesa Mustapha Zubairu.
Taron sauraren ra’ayoyi da shawarwarin jama’a wanda aka fara gudanar da shi a minna da ya shafi qananan hukumomin Rafi, Munya da Shiroro, Paikoro da Bosso a vangaren masarautar minna.
Sai taro kashi na biyu da ya gudana a garin Bida, da ya shafi qananan hukumomin Bida, Agaie, Lapai da Mokwa, Lavun, Edati da Katcha, Gbako da ya shafi masarautar Bida.
Hukumar ta sake shirya taron da ya shafi masarautar Kontagora da ya shafi qananan hukumomin Kontagora, Mariga, Mashegu da Bargu, Wushishi da Rijau, Magama ya samu halartar manyan sarakuna da qwararru a fannoni da dama inda suka tattauna tare da bada shawarwarin da suka da ce kan hanyar da za a bi a samu kundi daya da Gwamnatin jihar za ta turawa majalisar dokokin jiha dan amincewa da shi ya zama doka akan tsarin da gwamnati za ta yi anfani da shi wajen samar da tsarin inganta biranen jihar.
Tsarin wanda zai qunshi da barun inganta tattalin arzikin jihar da samun kudaden shigar gwamnati da samar da ayyuka ga din bin jama’ar jihar.
Da yake bayani a taron bude tattaunawar a fadar sa, mai martaba sarkin Suleja Malam Awwal Ibrahim yace masarautar Suleja tana kundin da ta tsara kan yadda za a ciyar da masarautar gaba, akwai buqatar wannan kwamitin da ta samu kwafin wannan kundin dan yin aiki da shi a cikin rahoton da za ta gabatar, yace masarautar Suleja na fuskantar matsaloli da dama kan rashin hanya da magudanan ruwa wanda ko a damanar bana da ya gabata sai da aka samu ambaliyar da ya janyo hasara mai xin bin yawa, sannan muna buqatar gwamnatin jiha da ta samar da dokar da za ta ba mu dama wajen kulawa da yadda harkokin kasa ke gudana saboda kwararan baqi da kusantar mu da babban birnin tarayya ya janyo ta yadda yara masu tasowa ba su koka akan rashin daukar matakan da suka da ce ba.
Hajiya Sa’adatu Bokane, ita ce mai baiwa gwamna shawara akan harkokin bude ido da al’adun gargajiya, ta janyo hankalin kwamitin da tayi dubi akan wuraren yawon shakatawa da ke jihar, inda tace lallai idan an samar da tsari ingantacce ko bangaren yawon bude ido da al’adun gargajiya za ta iya samar da kafar ayyuka da dama wanda zai baiwa jama’a aiki ta yadda gwamnati kuma za ta iya samun kudaden shiga.
Saboda haka ina baiwa kwamitin Farfesa Mustapha shawara, a bangaren masarautar Kontagora muna samar da man kwara, shinkafa da waken suya da sauran kayan abinci akwai bukatar wannan shirin na inganta birane da samar da ayyuka ga jama’a da su bullo da tsarin da zai baiwa manyan kamfanoni damar shigo wa yankin nan dan jama’a su anfana da su.
Da yake karin haske, kodinetan shirin samar da tsarin inganta birane a jihar Neja, Farfesa Mustapha Zubairu yace an qirqiro wannan shirin ne bayan wata gayyatar da mai girma Alhaji Abubakar Sani Bello ya samu daga UN-Habitat a wani taron da ta shirin kan tsarin inganta birane na duniya a kasar Faransa a watan Mayun 2017.
Inda aka tattauna kan yadda gwamnatocin kasashe zasu bullo da tsare-tsaren inganta manyan biranen kasashen su, wanda hakan ya baiwa gwamna kwarin guiwar ganin wannan tsarin bai tsaya a cikin manyan garuruwan ba kadai ya karade dukkanin kananan hukumomin jihar nan, kan haka muka zabi ziyartar jama’a dan tattaunawa da su hanyoyin da za a bi wajen inganta birane da al’adu ta fuskar cigaban da zai bada damar anfana da shi wajen samar da ayyuka ga jama’a da kuma samun kudaden shiga ga gwamnati.
Farfesa yace yanzu haka ganin karamar hukumar Suleja na kusa da babban birnin tarayyar Najeriya akwai shirin samar da rukunin gidaje na musamman wanda har gwamnati ta samu fili hekta goma sha daya da za a fara gwajin wannan aikin rukunin gidajen kafin ya watsu a sauran sassan jihar.
Burin gwamnati akan wannan shirin shi ne baiwa masu hannu da shuni da kamfanoni damar zuba jari a dukkanin bangarorin da suka shafi samar da gidaje, hanyoyi, ayyukan yi ga jama’a dan bunkasa arzikin jihar ba tare da jiran kudade daga gwamnatin tarayya ba.
Dan haka yana daga jin jinan da za mu yiwa gwamnatin Koriya ta kudu a matakin farko na bada tallafi ga gwamnatin jiha dan ganin an soma gudanar da wannan shirin cikin lokaci, domin samar da tsarin inganta birane na jiha zai baiwa masu zuba jari kwarin guiwar shigo wa dan habbaka tattalin arzikin jihar nan daga matakin jiha har zuwa kananan hukumomi.