AN KAMA MACE CIKIN MASU GARKUWA DA MUTANI A NASARAWA

An kama wata mata da laifin yin garkuwa da mahaifiyar kawarta a Nassarawa

Daga Zubairu M Lawal

Rundunar Yansandan jahar Nassarawa ta sanar da kama wata mata yar shekara 29 mai suna Paulina Santos wanda ta hada baki da wasu miyagun mutane suka yi garkuwa da mahaifiyar kawarta.

Kamar yadda labari ya tabbata cewa mijin kawar Paulina ma’aikaci ne a kamfanin man fetir na Najeriya, NNPC. A yayin da Yansanda suka yi holen Paulina a babban ofishinsu dake garin Lafiya, kwamishinan Yan sanda Bola Longe ya yi ma manema labarai jawabi kamar haka .

Kwamishinan Longe ya ce a ranar 11 ga watan Feburairu suka kama Paulina Santos, kwararrun jami’an Yan sanda daga sashin yaki da sata tare da garkuwa da mutane ne suka yi nasarar cafketa.

Babban dan sandan ya ce Paulina wanda ta fito daga karamar hukumar Ogbadigbo na jahar Benuwe tana zaune ne a unguwar Azuba Bashayi, cikin karamar hukumar Lafia a yankin raya kasa ta Arewacin Lafia na jahar Nassarawa, kuma tana aiki da wata cibiyar karbar magani.

“Wanda ake zargi ta hada kai da wasu miyagu ne domin sace matar, kuma tuni ta amsa laifinta, mu kuma za mu gurfanar da ita gaban kotu da zarar mun kammala gudanar da bincike.” Inji shi.

Ita ma Paulina ta bayyana ma manema labarai cewa ta aikata laifin, amma tana neman gafara a kan cewa ba za ta sake sikata irin wannan aika aika ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *