An zargin mutum biyar sun kamu da cutar Korona bairos a Nasarawa
Kwamishinan lafiya
Daga Faruk Musa
Kwamishinan harkokin kiwon lafiya ta jihar Nasarawa Dakta Ahmad Baba Yahaya ya tabbatar da samun wasu mutum biyar da aka samu da cuta makamancin na Korona bairos.
Kwamishinan yace; mutanin da ake zargin ba a tabbatar da sashihancin cutar ba saboda yanzu an dauki jininsu an tafi dashi sashin binchike a Abuja, saboda a tabbatar da gaskiyar lamarin.
Yace; mutum biyar duk kaninsu yan gida daya ne. Yanzu an killace su an kuma kulawa da su a Asibitin Gwamnatin tarayya dake garin Keffi.
Ya kuma yi kira ga alumman jihar dasu kasance masu bin dokoki kamar yadda aka shigida. Cewar alumma su kasance masu mu’amala nesa nesa da kuma yawan tsaftace Hannaye.
Tun da farko dai Hukumomi a Asibitin Gwamnatin tarayya dake garin Keffi FMC a jihar Nasarawa sun tabbatar da killace mutane biyar yan gida daya da ake zargin sun kamu da cutar Coronavirus da ta addabi kasashen duniya.
Tuni dai an dau jininsu kuma an kai cibiyar takaita yaduwar cuta ta kasa NCDC dake Abuja domin gwaji da tabbatarwa.
Shugaban Asibiti, Dakta Yahaya Baba Adamu, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai ya ce mutane su kwantar da hankulansu , domin an dau matakin dakile yaduwar cutar ta ko ina.
Dakta Yahaya yace: “Gaskiya akwai yan gida daya a asibitin. Daya daga cikinsu ne ya fara nuna alamu, daga baya sai dukkan yan gidan suka fara nuna alamu irin nasa na zazzabi, mura da sauransu.”
“Amma tun da mutumin ya ziyarci jihar Legas da Ogun kwanakin nan. Mun yanke shawarar cewa a mayar da hankali kan lamarin kuma ya kamata a killaceshi.”
A cewarsa, mutane hudu cikin biyar da aka killace sun fara samu lafiya.
Yayinda aka tambayesa shin me zai faru ga ma’aikatan Asibitin da suka hadu da mutanen dake killace, Likitan yace: “Idan sakamakon gwajin ya nuna cewa suna dauke da cutar, zamu nemi ma’aikatan da suka hadu dasu.”